Malam Muhammadu Abbas shi ne dan Sarki Abdullahi Maje Karofi dan Sarki Malam Ibrahim Dabo. Malam Abbas mutum ne mai rangwame, mai adalci kuma masoyin jama’a.
A Ranar 2 ga watan Afrilu, 1903, Gwamna Lugga ya dawo daga Sakkwato kuma a ranar ne ya nada Wambai Abbas, ya kuma tabbatar da shí bisa gadon sarautar Kano. Aka yi kasaitaccen sbagali sosai.
A lokacin bikin, Gwamna Lugga da hannunsa ya mika wa sabon Sarki wuka da takobi, sannan ya bude masa laimarsa. Ita sandar sarautar da Gwamna Lugga ya mika wa Sarki Abbas irin sandar nan ce mai daraja ta daya, kamar wadda suka bai wa sabon Sarkin Zazzau. Daga nan, aka rako Sarki ya shiga gidan sarauta.”
Zaku Iya Karanta
Sarki Kano Abbas mutum ne wanda ya kware a sha’anin mulkin jama’a, mutum mai kaifin hankali da hangen nesa. Ya yi kokarin tabbatar da zaman lafiya a Kano da samun karuwar arziki da wadat. Sarki Kano Abbas ya zama mai biyayya, yana umurtar jama’a da su bi abin da zamani ya kawo.
Karanta
Ya nuna cewa shi makiyayi ne kawai, mutane kuwa su ne abin kiwo, don haka a nemi zaman lafiya a wannan zamani. Allah Shi ne mai zamani.
Zaku iya Karanta
Tun daga wannan shekara ta 1903 zuwa 1919, Turawa suka fitar da hakimai masu yawa. Hakan ya zama dole, domin su tabbatar da mulkinsu a kan mutane. Ta haka ne za a bi su ki-da-so, mulkin kasa yana hannunsu.
Misali, Sarkin Dutse da Dawakin Kudu da Dan’iya da Dan’isa mai ruwa da dan Danburan Cigari hakimin Minjibir da Birnin Kudu da Sarkin Dawaki ldrisu da Danlawan Amadu da Gurara hakimin Dutse da Turaki Manya da hakimin Kura.
Galibinsu yan’uwan Sarki ne, sai suka ce Sarki ya cike gurabansu, sai Sarki ya nada Umaru Galadima ya nada Salihi Turaki ya nada babban dansa Abdullahi Bayero Ciroma. Wadannan nade-nade duk a farkon zuwan turawa aka yi su.
Tun a farkon mulkinsa, Sarkin Kano Abbas ya kai wa Gwamna Lugga ziyara a hedikwatarsa ta Zungeru. Ya kuma yi wannan ziyara lafiya, ya kare ta lafiya, suka yi muhimman shawarrari da Gwamna Lugga ya dawo gida.
A zamanin Sarkin Kano Abbas, Turawa sun kawo wasu muhimman canje-canje a sarautar Kano. A lokacinsa ne aka kirkiro gundumomi inda aka tuttura masu hakimai da za su kula da su, maimakon tsarin da ake yi a da na dukkan hakimai suna tare da Sarki a cikin birni, sai dai a yi rangadi a dawo. A wannan lokaci ne aka gina wa hakiman gidaje a gundumominsu na mulki inda suka fita daga cikin birnin Kano suka koma kauyuka.
Karanta
Ta haka aka kekketa manyan kasashe wadanda ‘yan’uwan Sarki suke rike da su a da. Tun a lokacin Sarkin Kano Abbas, Turawan Mulkin Mallaka suka fara kafa makarantun koyarwa na zamani inda suka fara koyarwa ta wasu fannonin addinin Musulunci da kuma na boko, musamman koyar da rubutu da karatu na bakaken Romawa na boko.
muhadu a kashi na biyu