Wasu Abin Al’ajabi Da Amfanin Rakumi Wajen Kiwon Lafiya

0 441


“Ashe ba za su duba ga Rakumi yadda aka halittasu” suratul gashiyat aya ta 17.

Manzon Allah ﷺ ya umarci wasu mutane daga kabilar Uki ko Uraina su sha Nonon Rakumi da Fitsarinta bisa wani lalura na rashin lafiya da suke fama da ita {sahih Bukari 2855 sahih Muslim 171}.

Rakumi dai wata halittace daga cikin dabbobin da Allah madaukakin sarki ya halitta bisa hikima da ikonsa akwai ayoyi da hikimomi masu yawa tattare da irin tsari na musamman da Allah yakeɓanci raƙumi da su kuma ya halicci raƙumi da su domin su zamo ayoyi abin lura ga ma’abota hankali.

Rakum kasaitacciyar dabbace da Allah ya halitta domin ya iya biyan buƙatar al’ummar da suke rayuwa a ɓangaren hamada ana samunsu a kasashe da dama wasu kasashen saboda darajarta Gwamnatin kasar har ma’aikata take budewa don kula da su.

Rakumi kan iya rayuwa har na tsawon kwana takwas ba tare da ci ko sha ba sai yasa idan Raƙumi ya samu inda zai sha ruwa kasancewar yana da matuƙar bukatarsa sai ya sha ya kuma ajiye wani ruwan a cikinsa yakan iya shan Ruwan da ya kai ɗaya bisa uku na girmansa a cikin minti goma kacal kwatankwacin galan 30.

Halittar da Allah ya yiwa Rakumi daban take dana sauran dabbobii ta ababe da dama daga ciki sun hada da;

Ya kan iya rayuwa shi kadai a cikin sahara ba tare da sauran dabbobi ba.


Ya kan iya tafiya shi kadai a cikin kowane irin sahara ba tare da kafafunsa sun lume ciki ba.


Duk muguntar da kamai yana ramawa koamai daren dadewa.


In ransa ya baci yakan bar duk wani aiki da yake yi.


Duk da irin karfin da yake da shi amma yana tsoron kunama in ya hango kunama yana canja hanya yana gane cewa akwai kunama a guri tun kafin ya isa gurin.


Baya barbara wa jininsa kanwarsa ko yarsa.


Yana gane cewa akwai ruwa a guri tun kan ya isa da kusan mita dari.


Duk a cikin dabbobi ba wanda ya kai shi hakuri da kawaici.


Baya mantuwa koda shekara nawa abu zai kai baya manta uwarsa da sauran yan uwansa.


A duk dabbobin da Allah ya halitta Rakumi ce kadai komai nata yake da amfani tun daga kan namansa fitsarinsa kashinsa fatarsa nononsa sai yasa ma fitsarin ba najasa bane kuma haram bane akan iya sha ko a shafa don wata lalura.


Allah ya mai murfi a gaban idanunsa wanda duk tashin kura a sahara baya kaiwa ga idanunsa ba tare da ya rufe idanunsa.

Fitsarin Rakumi

Abu Kilaba ya ruwaito hadisi daga Anas bin Malik R.A ya ce “wasu mutane daga kabilar Ukl ko Uraina sun zo madina sai yana yin garin bai musu ba {sun samu cangin yanayi} rashin lafiya ya kamasu Manzon Allah ﷺ ya umarcesu da su sami inda Rakumi yake su sha Nonon sa da fitsarin sa {a mazaunin magani} suka je suka sha bayan sun sha suka sami lafiya sai suka kashe mai Rakumin suka gudu da Rakuman Manzon Allah ﷺ yasa aka kamo su ya musu hukunci” ingantaccen hadisine Bukari ya fitar a Hadisi mai lamba 2855 Muslim a Hadisi mai lamba 1671 Hadisan da suka yi magana akan amfanin shan fitsarin Rakumi da Nonon sa suna da yawa likitoci sun yi bincike kuma sun tabbatar da hakan.

Ibnul Kayyim ya ce “Mawallafin Littafin kanun Ibn Sina ya ce fitsari mafi amfani shine fitsarin Rakumi da ake kiranta Najeeb” Zadul Ma’ad juzu’I na 4 shafi na 47 zuwa 48.

Jaridar Emirati mai lamba 11172 wacce ta fito a shekarar fabairu 2006 ta rubuta wani bincike da tayi akan Rakumi inda ta kawo cewa abu mafi amfani da yake jikin Rakumi akwai nononta yana tasiri wajen maganin ciwon zuciya da narkar da abinci da cututtuka da suka shafi daji da sauran cutuka.

A wani bincike da ya yi Dr Ahlam al~awadi wanda magazine na al~da’awa suka buga mai lamba 1938 a shekarar 2004 ya ce akwai amfani mai yawa a cikin nonon Rakumi daga cikin abun da ya kawo ya tabbatar da cewa fitsariin Rakumi na yana taimakwa wajen maganin cutar da ta shafi fata yana gyra ga shi ya sanya shi kyalli da laushi ya kuma fidda amosanin kai.

Mawallafan litatafin al’ibl asrar wa’ijaz {rakumi sirrukanta da ijazozinta}Darman Ibn Abdul Azeez da Ibn Mudlak alsuba’iy sun tabbatar da cewa fitsarin rakumi nada amfani sosai kamar yadda Manzon Allah s.a.w ya fada da kuma bincike na zamani sun tabbatar da cewa fitsarin Rakumi nada tasirin wajjen magance abubuwan da kan iya jawo cutuka a jikin dan adam sun ci gaba da cewa mata na amfani da fitsarin Rakumi wajen wanke kai don ya kara musu gashi ya sa shi haske da laushi.

Dan uwa ko yar uwa mu rika amafni da wannan dabbar saboda albarkar da Allah ya mata.

Mu hadu a rubutu na gaba don jin Amfanin Nonon Rakumi da Fitsarin sa.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »