Bani Da Lafiya Kashi Na Tamanin Da Tara (89)

0 475

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Malama tana kammala bayanin nan ne sai matar tayi godiya matuka da gaske sai takara tambayar malamar tana cewa: Shin Malama iya wadan nan ma kadai sun wadatar ko akwai wasu nau’o’in shawarwarin da ake iya amfani da su a wannan gurbin?

Malama: Eh kwarai kuwa akwai, na farko dai a koyawa yara su saba da karanta Alqur’ani da Azkaar na safiya da maraice da lokacin kwanciya barci, da lokacin da fita da shigowa gida, da shiga ban daki da fitowa da Lokacin cin abinci da kammalawa, kuma da zarar magariba ta yi a daina sakinsu suna shiga ko ina a rika tsare su a wuri daya.

Matar: To malama lokacin magriba din nan fa muna aikace-aikacen gida kuma yaran muna sakinsu ne suje suyita yin wasanninsu don su bamu sarari muyi ayyukan mu cikin nutsuwa.

Malama: Allah sarki, ai lokacin magriba lokaci ne da shedanun Aljanu suke yawaita zirga-zirga a cikin mutane, kuma suna matukar yiwa yara illa a daidia lokacin ga duk yaron da ake sakinsa yana fita wasannin magriba kafin magriba ko bayanta, kuma Annabi Sallallahu alaihi Wasallama ne yayu mana umarnin kar mu rika sakin yaranmu a daidai wannan lokacin.

Maman Sultan dai tayi tagumi tayi jugumm ta kasa cewa komai, sai ta shiga tunanin zuci tana cewa: Allah mai iko, ka ji yadda ake yin abu nan cikin sauki ba wahala ba kashe ko sisi, Allah kara yafe mana kusakuranmu da muka gabatar kuma ya kara tsare mana imaninmu.

Sai Ummu Labeeba taga yanayin da Maman Sultan take ciki sai ta fahimci anya lafiya kuwa….

Sai ta dafa kafadarta tana cewa: Maman Sultan lafiya kuwa?

Maman Sultan ta farka a firgice, sai ta kama shasshare hawayen dake a fuskarta tana cewa: Ba komai yar uwa, kawai dai damuwa ce tayimin yawa sosai akan wadanda na kai su wajan bokaye Allah ne kadai yasan adadin yawansu, na hallakar da su, na batar da su, ni yanzu ma na rasa yadda zanyi.

Ummu Labeeba itama dai tausayi ya kama jikinta tana cewa: Ai yar uwa, karkiji komai, Allah kika sabawa kuma yana matukar nuna so, farin ciki tare da maraba ga duk wanda yake neman gafarar da yafiyarSA, kuma In sha Allah zai gafarta miki ya yafe miki kuskauranki.

Maman Sultan: Tayi murmushi tace: Alhamdulillah kuna ganin zai gafarta min kuwa, saboda laifina fa babba ne saboda Shirka ne Mu’amila da bokaye?

(Insha ALLAH za muji ci gaban lamarin a rubutu nagaba.)

Allah yasa mudace Kuma yakara mana lafiya mai amfani.

Har kullum mu rika tabbatarwa da zuciyar mu cewar: Magani sila ne na waraka amma ba shi da ikon warkarwa, Allah ne kadai mai iya warkar da wanda yaga dama a duk lokacin da yaga dama, shi kadai ne abin dogara ba maganin ba.

(Ayi mana Addu’ar ALLAH ya yarda da mu da ayyukanmu kuma ya lullube mu da RahamarSA.🤲🏻)

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »