Allah Ɗaya Gari BanBan Kashi Na Biyu (2)

0 285

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Cigaba……..

Zan jinkirta maka har sa’adda Allah ya hore maka, ka kawo mini kifi na adadin kuɗin da nake bin ka.”

Masunci ya karɓi gurasa da kuɗi ya yi godiya, ya kuma ce wa mai gurasa, “Allah ya saka maka da alheri, ya taimake ka kamar yadda ka taimake ni.” Ya sayi abin da yake buƙata na cefane, ya nufi gida cike da farin ciki.

Da isarsa sai ya tarar da matarsa zaune, yara sun zagaye ta suna ta kuka saboda yunwa, ita kuwa tana rarrashinsu tana cewa, “Ku yi haƙuri mahaifinku na nan tafe da abin da za ku ci yanzu.” Ya kawo gurasa ya ba su suka ci har suka ƙoshi. Ya kwashe labarin abin da ya faru gare shi duka ya faɗa wa matar. Ta girgiza kai cikin mamaki ta ce, “Allah shi ne mai baiwa.”

Washegari Abdullahi ya saɓa koma ya nufi teku yana cewa, “Ya Allah ka nufe ni da kamo abin da zai faranta fuskata da ta mai gurasa.”

Yana isa bakin teku ya warware raga ya watsa cikin ruwa. Sa’adda ya jawo ta tudu, bai tarar da kifi ko ɗaya a ciki ba. Haka ya yi ta yi har zuwa faɗuwar rana bai kama komai ba. Ya naɗe koma ya nufi gida cike da baƙin ciki, ga shi kuma hanyar da zai bi dole sai ya bi ta gaban rumfar mai gurasa. Ya ce a ransa, “Idan zan wuce ta gaban rumfar sai in ƙara sauri, kada mai gurasa ya hango ni.”

Lokacin da ya yi kusa da rumfar, sai ya hangi mutane maƙil a ciki, don haka sai ya sunkuyar da kansa ƙasa, yana jin kunyar haɗa ido da mai gurasa, ya ƙara mai, wai don ya wuce ba tare da mai gurasa ya gan shi ba. Sa’adda ya zo daidai ƙofar, sai idanun mai gurasa suka faɗa kansa, ya ɗaga murya ya kira shi, “Taho mana, ya kai masunci. Shin ka manta da gurasarka ta yau da kuɗin cefane?”

Abdullahi ya amsa masa, “Wallahi ban manta ba, ina jin kunyar zuwa gare ka saboda ban kama kifi a wannan rana ba.”

Mai gurasa ya yi murmushi ya ce, “Kada ka ji kunya. Ban ce maka sai sa’adda Allah ya hore za ka biya ni ba.” Ya kawo gurasa da nusufi goma ya ba shi.

Masunci ya tafi gida ya faɗa wa matarsa abin da ya faru. Ita kuma ta ce, “Ba komai, Allah mai baiwa ne! Da sannu za ka samu abin da za ka biya mai gurasa, in sha Allah!”

Masunci bai gushe ba, tsawon kwanaki arba’in, yana zuwa bakin teku kullum, tun hudowar rana har faɗuwarta, amma Allah bai nufe shi da kama kifi ko ɗaya ba. Kuma kullum sai mai gurasa ya ba shi gurasa da nusufi goma na cefane ba tare da ya taɓa canja masa fuska ko ya tambaye shi kifi ba. Bai kuma taɓa ƙyale shi yana jira kamar yadda yakan yi wa sauran mutane ba.

Za mu ci gaba, in sha Allah.

Marubuci

Bukar Mada

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »