Sarkin Kano Abdullahi Maje Karofi (1855-1882)

2 1,388

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Malam Abdullahi, Maje Karofi, shi ne dan Sarkin Kano Malam Ibrahim Dabo Basullube. Shi ma Malama Shekara ta haife shi, kuma an sa masa sunan Malam Abdullahi Danfodiyo wato Abdullahin Gwandu.

Malam Abdullahi, mutum ne dogo, mai kwarjini, mutum mai himma, mai kwaz0, mai alkawari da rikon amana, jarumin gaske da zabura a kan makiya masu tayar da alkawari da masu taurin kai.

An nada Malam Abdullahi Maje Karofi ya zama Sarkin Kano na hudu a daular Fulani bayan rasuwar wansa, Sarki Usman dan Dabo, a shekarar 1855. Malam Abdullahi sarki ne jarumi wanda ya dada inganta mulkin Kano ya kara kyautata shi.

Sannan yana daga cikin sarakuna wadanda suka dade a kan gadon mulki. Sarki Abdullahi ya tsai da mulki mai karfi irin na mahaifinsa Malam Ibrahim Dabo. Shi ya sa ma ake masa kirari da cewa, ‘Abdullahi dagi maganin kasa mar tsauri.

Sarki Abdullahi, sarki ne wanda yake shiga kayan sarauta ya yi sunkun da shi inda zai nada katon rawani da kunnuwa biyu da amawali da hunu, kamar yadda Dabo yake yi. Ya kuma shiga kokuwar alkyabba, yana rataye da takobi da wukar yanka wadda Shehu ya ba su.

Hakika, Sarkin Kano Abdullahi ya mike kafarsa har ya nada sarautu” sosai wadanda suka taimaka masa wajen gudanar da mulkinsa.

Sarkin Kano Abdullahi idan ya hau karagar mulki zai fara shari’a yakan daga yatsarsa sama ya ce, “Wallahi tallahi zan taka shiKo da dana ne, dukkan wanda na samu ya taka shari’a.”

A lokacin mulkinsa, Sarki Abdullahi ya zartar da hukuncin kisasi da kuma haddi wato wanda ya kashe wani da ganganci shi ma a kashe shi.

Kuma an yi wa barayi hukunci daidai da su inda ya rika yanke nannun barayi, kamar yadda Allah, Madaukakı, ya yi umurni.

Shi ya sa ake kiran sa ‘Abdu Sarkin Yanka.’ Shi ne ya fara kafa kwamitin zakka wanda yake kula da karbar zakka da rarraba ta ga wadanda suka dace.

Sarkin Kano Abdullahi kuma ya kafa baitulmali inda ake ajiye kudin hukuma don taimaka wa gajiyayyu da musakai da gudanar da sauran bukatu na daular Musulunci.

Abdullahi Maje Karofi ya yi fama da tawaye na wasu sassan Fulani da kuma yake-yaken da suka faru tsakanin Fulani da Umbutawa da wasu sarakunan Maradi kamar Sarki Danbaskore da sauransu.

Har wa yau, Sarki Abdullahi ya yi wasu ayyuka da suka hada da gina Masallacin Turaki Manya, ya kuma gina Soron Giwa da dan Takai wanda aka mayar da shi sansanin yaki.

Shi ne ya gina Gidan Birnin Bako domin yaki da Umbutawa. Gidan Nasarawa da Haka kuma Sarki Abdullahi Maje Karofi ya tafi Sakkwato ya kai ziyara inda ya bar dansa Yusufu a matsayin wakilinsa a Takai.

Bayan tafiyarsa, sai Haruna Danmaje Ba’umbuce ya kai wa Yusufu dan Maje Karofi harin yaki. Aka yi mummunan yaki, Kanawa suka fashe suka bar Yusufu. Ba don Allah ya sa Yusufu yana da gwanintar yaki ba, da bai tsira ba.

Da sarki ya dawo gida ya ji labarin abin da ya faru tsakanin Yusufu da Haruna Danmaje, sai ya nada Yusufu Galadimah Kano. Daga nan ma ya sake tura shi zuwa Maguzawan Dala don neman Haruna Danmaje, a inda suka gamu a Jambo suka yi yaki, Yusufu ya yi nasara mai yawa ya dawo gida.

Sarki Abdullahi Maje Karofi bai zauna wuri daya ba, a tsaye yake, yakan tashi daga wannan gari zuwa wancan. Ya san ko’ina a cikin kasarsa.

Jarumin sarki ne, kuma uban marayu da gajiyayyu Sannan an sami ci gaba a zamaninsa, Kano ta bunkasa sosai, musamman ta hanyar cinikayya. Kuma addinin Musulunci ya dada inganta, ya sami daukaka da bunkasa.

Sarki Abdullahi bai zauna ba sai da ya ga ya kafa mulki mai adalci, kasa ta yi daidai.

Abdullahi Maje Karofi ya rasu a cikin shekara ta 1882 a yayin da zai tafi Sakkwato gai da Sarkin’Musulmi kamar yadda ya saba a kowace shekara. Allah ya gafarta masa.

[review]

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

  1. […] Sarkin Kano Abdullahi Maje Karofi (1855-1882) […]

  2. […] Sarkin Kano Abdullahi Maje Karofi (1855-1882) […]

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »