Ƙirƙirar Jihohi A Nijeriya (1967-1996)

0 433

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Nijeriya ta kasance tana gudanar da tsarin yanki tun daga shekara ta 1960 zuwa shekara ta 1966. Tsakanin shekara ta 1967 da shekara ta 1996, an kasa ƙasar zuwa Jihohi talatin da shida (36).

Gwamnatin Nigeriya ta yi aikin samar da jiha na farko ne lokacin shugabancin Yakubu Gowon a shekara ta 1967. Kafin hawan Gowon mulki, Aguiyi Ironsi ne shugaban soja na farko a Najeriya. Bayan kashe shi a watan Yulin 1966, Gowon ya zama sabon shugaban mulkin soja na kasar.

A ranar 5 ga watan Mayu, 1967 Shugaba Gowon ya wargaza yankuna hudu na ƙasar sannan ya ƙirƙiro Jihohi goma sha biyu (12). Jihohi shida sun kasance daga tsohon yankin arewa. Su ne: Jihar Arewa maso Yamma, Jihar Arewa maso Gabas, Jihar Kano, Jihar Arewa ta Tsakiya, Jihar Benue-Plateau da Jihar Kwara. Tsohon yankin yamma ya rabuzuwa Jihohi biyu: Jihar Yamma da Jihar Legas. Tsohon yankin tsakiyar yamma ya zama Jihar Yamma ta Tsakiya, yayin da tsohon yankin gabas ya dare zuwa Jihohi uku. Waɗannan su ne Jihar Gabas ta Tsakiya, Jihar Ribas da kuma Jihar Kudu-maso-Gabas.

A shekara ta 1976, biyo bayan hamɓarar da gwamnatin Yakubu Gowon a juyin mulkin da sojoji suka yi wadda yayi sanadiyar zuwan Murtala Mohammed a matsayin shugaban ƙasa, Murtala ya kirkiro jihohi kamar haka: Anambra, Bauchi, Benue, Imo, Niger, Ogun da Ondo, wanda ya kawo jimillar Jihohi suka zama goma sha tara (19) daga Jihohi goma sha biyu (12) da Gowon ya kirkira.

An ɗauki tsawon shekaru goma sha ɗaya (11) ba tare da ƙirƙirar wata Jiha ba sai a shekara ta 1987 wato a karkashin mulkin IbrahimBabangida (1985 – 1993).

A shekara ta 1987, Babangida ya ƙirƙiri Jihohi biyu (2), wato Akwa Ibom da Katsina. Ya kuma ƙirƙiro ƙarin Jihohi tara (9) a shekara ta 1991. Waɗannan su ne: Abia, Enugu, Delta, Jigawa, Kebbi, Osun, Kogi, Taraba da Yobe.

Yana da kyau a lura da cewaan cire Jihar Akwa Ibom ne daga Jihar Kuros Riba, sai Jihar Katsina daga Jihar Kaduna. Hakazalika an cire jihohin Adamawa da Taraba daga tsohuwar Jihar Gongola, da kuma Jihar Enugu daga Jihar Anambra, yayin da jihohin Edo da Delta suka maye gurbin tsohuwar jihar Bendel. Har ila yau, an ƙirƙiro Jihar Yobe dagaJihar Borno, da Jigawa daga Jihar Kano, yayin da jihohin Kebbi da Osun aka ciro su daga Sokoto da Oyobi da bi. Jihar Kogi ta fito ne daga jihohin Kwara da Binuwai.

A shekara ta 1991 jimillar Jihohin Nijeriya ya zama talatin (30).

Sani Abacha ya zama shugaban mulkin soja na Najeriya a shekara ta 1993 bayan hamɓarar da gwamnatin wucin gadi ta ƙasa wanda shugaba Ernest Shonekan yake jagoranta.

Saboda tsananin tashin hankali ga ƙarin Jihohi, Abacha ya shirya Taron Tsarin Mulki na Ƙasa (NCC) wanda ya bada damar yin wasu abubuwa ciki har da ƙirƙirar sabbin Jihohi.

Don haka,a ranar 1 ga watan Oktoba, 1996, ya ƙirƙiro wasu jihohi shida, wato Ebonyi daga jihohin Abia da Enugu, Bayelsa daga Jihar Ribas, Nasarawa daga Jihar Filato, Gombe daga Bauchi, da kuma Ekiti daga Ondo.

An tsara jadawalin Jihohin da shugabannin da suka ƙirƙiresu da kuma shekarun da aka ƙirƙere su domin sauƙaƙa wa mai karatu, duba hoton da yake ƙasa domin ganin jadawalin.

Kirkirar jahohin najeriya

Yakubu Ahmad Yaya
10/09/2022

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »