Tarihin Sarkin Kano Muhammadu Abbas (1903-1919) kashi na 2

0 913

Daga cikin mutanen da aka fara koyarwa a irin wadannan makarantu akwai Abdulkadir dan Sarkin Kano Abbas duk da yake kuwa ya girma har ma yana rike da wata sarauta ta hakimi. Amma sai aka buga misali da shi don a tauna tsakuwa, aya ta ji tsoro.

Har wa yau dai a tsare-tsaren da Turawa suka kawo a zamanin Sarkin Kano Abbas yin kasashe na hakimai kamar haka:

  • A 1908 Birnin Kudu ta zama hakimi inda aka nada Sarkin Kudu NuHu.
  • Gwaram kuwa wadda a da take rike da Birnin Kudu ta koma cin gashin kanta kawai.
  • A 1908 dai kuma aka yi wa Bichi gunduma. Abdullahi Bayero wato Ciroman Kano ya zama farkon hikiminta.
  • Dawakin Tofa kuma kasar Madaki Usaini ta zama gunduma ita kadai.
  • A 1916 Gwarzo ta zama gunduma a karkashin Sarkin Dawaki Maituta Muhammadu Nata’ala.
  • Karaye kasar Sarkin Karaye Usman ta koma ita kadai.
  • Rano kasar Autan Bawo ta koma ita kadai a matsayin Gunduma.
  • A 1908 Tudun Wada ta zama gundüma kuma Dankadai ya zama hakiminta na farko.
  • A 1908 dai kuma aka hade Lardin Kano da Katsina da Katagun da Kazaure da Daura da Gumel da Hadeja da Misau da Jama’are da Ningi. Aka mayar da Kano ta záma cibiyar mulkinsa.

Amma daga baya an dauke Katagum da Misau da Jama’are da Ningi suka koma Bauchi wadda ta zama cibiyar mulkins.

Karanta Tarihin Sarkin Kano Muhd Abbas Na 1

Haka kuma a wajen 1911 jirgin kasa ya iso Kano a dai zamanin Sarkin Kano Abbas inda mutanen Kano masu yawa suka dinga fita zuwa kallon sa a Dan’agundi.

A zamanin Sarkin Kano Abbas ne aka yı wani babban taro cikin shckara ta 1912. A wannan shekarar ne kuma aka fara gina kasuwanni cikin tsarin layi-layi, maimakon rumfuna barkatai babu tsari, aka karu da ni’imomi masu yawa.

Sarkin Kano Abbas kuma ya sami yan majalisa, malamai masu gaskiya da tsoron Allah wadanda kuma suka yarda da abin da Allah ya kawo dangane da zamani su ne kuma:

Karanta

  • Galadima Umaru
  • Wambai Usman
  • Madaki Hussaini
  • Makama Majeli
  • Sarkin Bai Abdulkactir
  • Sarkin Dawakin Tsakar Gida ldrisu
  • Waziri Sarki
  • Waziri Alabar Sarki (Turgwa)
  • Turaki Salihi
  • Ciroma Abdullahi Bayero
  • Galadima Abdulkadir
  • Barde Abdu na Gwangwazo
  • AIkali Gidado Waziri (daga baya ya zama Wazirin Kano)

Karanta

A Zamanin sarautar Sarkin Kano Abbas ya ta6a kai ziyara kabarin mahaifinsa, Sarkin Kano Abdullahi Maje Karofi da yake a garin Karofi. Sarkin Kano Abbas ya yi wannan tafiya ne tare da amincewar Gwamna Janar, wato Gwamna Lugga. Sarki ya je ya yi wannan ziyara ya dawo lafiya.

Mulkin Sarkin Kano Abbas ya sami nasara sosai, Kano ta Kara bunkasa ta kowane nau’ina rayuwa. Jama’a sun saki jiki sosai suka ci gaba da harkokin cinikayyarsu Noma da kiwo suka dada bunkasa, kuma ga shi babu sauran yaki, Turawan Mulkin Mallaka Sun kuma hana bauta bullantana a sayar da da makwabtansa, harkoki da ma’amaloli, na tsakanin Kasa da kasa suka dada ingantuwa.

Kano ta sami arziki da alhaira suna ta bullo mata ta kowane gefe.

Allah ya yi wa Sarkin Kano Muhammadu Abbas Maje Nasarawa rasuwa a shekara ta 1919.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »