Bani Da Lafiya Kashi Na Tamanin Da Bakwai (87)

0 503

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

“Ku rika nemarwa kanku da iyalanku kariya daga sharrin halittun Allah ta hanyar da Shari’ar Muslunci ta amince da shi, matukar kuna son Allah ya jibinci lamurranku.”

Sai matar tace: Malama dalilin da yasa nayi wannan tambayar shi ne: Akwai wata kawata ce, ta zo da yaronta dan shekara 2 sai naga an rataya masa zobe na azurfa a wuya, da kuma wani awarwaro shi ba mace ba kuma, na tambayeta sai tace: Ai maganin mayu ne da masu kambun-baka, har take cemin wai nima ko za ta karbomin ne na rika sanyawa yara na?

Ni dai abin bai kwanta min a rai ba gaskiya sai nace mata: A’a ba yanzu ba tukuna zanyi dai shawara daga baya zan tuntube ki.

Wato Malama lamarin ne ni yake ta yimin kai-komo a zuciyata, na kasa samun natsuwa, shine nake so nasamu mafita wacce ta dace da shari’ar Allah kuma wacce hankalina zai kwanta da ita.

Sai Malama ta amsa mata da cewa: Subhanallah! Wato abinda ake ta fama da shi kenan ai yar uwa ba yanzu ba tun a zamanin baya, ana rataya wa yara azurfa a wuya, ko a daura musu wani zare a kugunsu da makamancin haka, wai nan da sunan tsari ko kariya, wannan kuma sam ba haka Addini ya koya mana ba, ya sabawa tafarkin Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama.

Saboda Addinin Musulunci ya haramta mana dogara da wanin ALLAH akan abinda Allah ne kadai zai iya yinsa, kuma yawanci irin magungunan nan za kuga babu komai a cikinsu sai shirka da sabon Allah, Saboda haka sai a kiyaye.

Matar tace: To Malama tunda har hakan ta kasance shi wanann din ba shi da kyau, to wannene wanda Shari’ar Musulunci ta amince amma muyi sai muyi shi, don tsira da Imanin mu da kuma mutuncin mu?

Malama: Ai Babu abinda Annabi Sallallahu alaihi Wasallama ya rage baiyi mana bayaninsa ba, wanda zai amfane mu face ya nusasshe mu gare shi, wanda zai cutar da mu kuma sai ya ankarar da mu da mu guje shi.

Allah yasa mudace Kuma yakara mana lafiya mai amfani.

Har kullum mu rika tabbatarwa da zuciyar mu cewar: Magani sila ne na waraka amma ba shi da ikon warkarwa, Allah ne kadai mai iya warkar da wanda yaga dama a duk lokacin da yaga dama, shi kadai ne abin dogara ba maganin ba.

(Ayi mana Addu’ar ALLAH ya yarda da mu da ayyukanmu kuma ya lullube mu da RahamarSA.🤲🏻)

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »