Tarihi
 
Tarihi wani muhimmin abu ne,wanda yake bawa al’umma damar sanin wani abu da ya wuce a baya hausawa kan ce kunne ya girmi kaka wato yaro da aka haifa kwanannan zai iya sanin abunda kakansa ma bai sani ba ko kuma ba a haifeshi  ba sanda abun ya faru.
 Idan muka duba wannan karin magana za mu ga cewa tabbas tarihi yana da amfani tunda zai baka dama ka san abun shekara da shekaru.
Dukkan wata al’umma da ba ta damu da tarihi ba to ba shakka tana cikin matsala saboda ba zasu san su waye su ba.
Ana sanin tarihi ta hanyoyi da dama kamar:
    1. Rubutu
    2. Faɗarsa da baki
    3. Amfani da kayan zamami
A cikin waɗannan hanyoyi ingantacciya kuma tabbatacciya ita ce hanyar rubutawa.
larabawa suna cewa ما كتب قررا وما حفظ فررا Wato rubutacce tabbatacce ne haddatacce kam ɓatacce ne.
Idan ba’a rubuta abu ba ta tabbas wata rana ana iya neman sa a rasa.
Translate »