Wani lokacin sai kaga ma’aurata na zamansu lafiya haka kurum sai ka rika ganin rikici yana kunno kai kalakala a tsakaninsu, ko kaji ita macen tana neman mijinta ya sake ta saboda ta tsanesa ba tare da wani dalili ba, ko taji ma zaman gidan ya ishe ta kuma idan ta fita unguwa sai taji ba komai a ranta har mararin gidan mijij takeyi, za tayi ta yiwa mijin wulakanci kala-kala amma daga baya sai tayi ta nadamar yin haka, kuma a baya ba halinta bane.
Dga cikin manyan dalilin nan su ne kamar haka:
1- Yin bacci tsirara ba tare da rufe al’aura ba.
2- Yin bacci da janaba a jikin mutum ( Ko da mutum baison yin wanka a daren to ya kamata ya tsaftace jikinsa kuma yayi alwala, da Asubah sai yayi wankan domin kwana ba tare da tsarki ko tsaftace janaba ba to akwai damuwa.)
3- Kallon madubi ba tare da yin Addu’ar kallon madubin ba, ko kallon madubi da daddare domin yin kwalliya ko haka kurum.
4- Rashin yin Addu’a yayin cire tufafi ko sauyawa ( Akalla mutum yace : Bismillah).
5- Shiga Bandaki (Toilet) ba tare da yin Addu’a ba.6- Yawaita magana da kunnawa da sauraron kade-kade da wake-wake alhali kana cikin banɗaki ( Toilet).
7- Yawaita yin kuka a wurin da yake da duhu.
8- Kallace-kallacen finafinan na batsa karanta littafai ko labaran batsa, ko hirar batsa a waya ko a zahiri.
9- Mutum yarika yin bacci shi kadai a cikin daki ba tare da yin Addu’a ba.
10- Yin rawa a gaban madubi musmaman da dare.
11- Mutum yarika yin tsirara a gaban madubi ko yayita daukar kansa video a tsirara.
12- Rashin yiwa juna Addu’a. Da rashin yin Azkaar na safe da yamma da na kwnaciya bacci.
13- Yawaita yada sirrin gidan miji ko duk abinda miji yasiya mata ko yayi mata sai ta sanar da kawaye ko ta yada a duniyar social media.
14- Saduwar aure ba tare da yin addu’ar da Annabi Sallallahu alaihi Wasallama ya koyar da mu ba.
15- Rashin karanta Alqur’ani ko sauraronsa.
Wadan nan kadan kenan daga cikin manyan dalilan da suke sanya Jinnul Aashiq shiga jikin mutane musmaman ma ma’aurata, tayadda zai rikita zamantakewar su, surika samun sabani akai-akai har wani lokacin ma a rabu.Amma akwai wadanda suke shiga tsakanin ma’aurata ta sanadiyyar Sihiri wasu ko wata tayiwa Ma’aurata sihirin rabuwa amma duk babu abinda zai iya samun mutum ko wani bawa sai DA YARDAR ALLAH.
Allah yasa mudace Kuma yakara mana lafiya mai amfani.
Har kullum mu rika tabbatarwa da zuciyar mu cewar: Magani sila ne na waraka amma ba shi da ikon warkarwa, Allah ne kadai mai iya warkar da wanda yaga dama a duk lokacin da yaga dama, shi kadai ne abin dogara ba maganin ba.
Ayi mana Addu’ar ALLAH ya yarda da mu da ayyukanmu kuma ya lullube mu da RahamarSA.

Domin Ƙarin Bayani Game Da Darrusan Marubucin.
+2348031542026
https://t.me/Rismawymedicine
rismawy86@gmail.com