Surorine guda biyu wadanda a jerin surorin ALQUR’ANI su ne na karshe lamba ta 113 da kuma ta 114.
Surorine wadanda ke qunshe da neman tsarin ALLAH daga dukkanin sharrin shaidanun mutane da Aljanu da dukkanin sharrin halittun Allah na zahiri da badini.
Surorin nan riga-kafi ne ga wanda shedanu basu taba shi ba, kuma waraka ne ga wanda sharrin shaidanu suka taba Da YARDAR ALLAH. Duk wanda ya dukufa da karanta su to tabbas zai samu tagomashi, kariyar ALLAH daga dukkanin abubuwan da yake jima tsoro, Kuma ALLAH zai bashi kariya daga dukkanin sharrin HalittunSA.
Shiyasa Annabi Sallallahu alaihi Wasallama ya kwadaitar da mu karatun ta a kullum kamar haka:
- Bayan kowacce sallar farilla ka karanta su da suratul Ikhlas sau 1, bayan sallar Asubah da Magriba a karanta su sau 3.
- Da safe da yamma, a karanta su sau uku-uku.
- Idan mutum ya kwanta zaiyi bacci sai ya haɗa hannuwansa biyu ya karanta Ikhlas, falaqi da Nasi har sau uku sai ya tofa ko ya hura a hannunsa sai ya shafa a jikinsa iya inda hannunsa zai kai.
Duk wanda yake karanta wadannan surorin kullum a yadda aka jero su din nan, to Tabbas Allah zai bashi kariya daga Dukkanin abubuwa kamar haka:
- SIHIRI ( tsafi, maita, yan kungiya).
- Kambun baka da Hassada.
- Shafar Aljanu da sauransu.
Allah ysa mudace.
Mu hadu a rubutu nagaba.
Allah yasa mudace Kuma yakara mana lafiya mai amfani.
Har kullum mu rika tabbatarwa da zuciyar mu cewar: Magani sila ne na waraka amma ba shi da ikon warkarwa, Allah ne kadai mai iya warkar da wanda yaga dama a duk lokacin da yaga dama, shi kadai ne abin dogara ba maganin ba.
(Ayi mana Addu’ar ALLAH ya yarda da mu da ayyukanmu kuma ya lullube mu da RahamarSA.🤲🏻)
Domin karin bayani:

Domin Ƙarin Bayani Game Da Darrusan Marubucin.
+2348031542026
https://t.me/Rismawymedicine
rismawy86@gmail.com