Ummu Bareerah tace: Wato Ummu Labeeba ina ji fa shiyasa a yanzu yawancin cututtukan da yara ke fama da su wadanda ake rasa gano ainihin abinda ke damunsu din nan, anya ba sa da nasaba da Kambun-baka wanda malama ke bayaninsa kuwa?
Ummu Labeeba: Ai kinsan yanzu abinda malama ke fadakarwa akai ya zama ruwan dare a wurin mutane, da zarar an haifi yaro ko uwar bata dau yaron hoto ba, to sai kinga yan uwanta ko yan uwan mijin ko ma wasu can dabam suna daukar jaririn hoto suna yadawa duniya.
Ummu Bareerah: Kuma fa kinga basusan iya nisan da hoton zaiyi ba kuma ba a san suwa da suwaye za su kalla ba, tunda kowa zai iya kallo Kuma ya tanka yaron a cikinsu har da masu Hassada da masu Kambun-baka. Allah da ya kyauta.
Ummu Labeeba: Ameen, ai wallahy sha’anin social media din nan, wasu suna wasarere da lamarinta, kuma ba karamin matsala take haifarwa ba fa, domin wasu ma a nanne suke haduwa da masu Kambun-baka ko aljanu.
Maman Sultan dai tayi shiru tana ta kallonsu tare da sauraronsu, ta kasa cewa komai saboda abin mamaki yake ta bata, saboda ta ga irin rayuwa cikin nutsuwa ba irin wacce take ciki a baya ba.
Sai wata mata tai tambaya tana cewa: To Mallama dangane da samarwa yara riga-kafi ko kariya daga sharrin Kambun-baka, Mayu ko dai wasu miyagu, shin zan iya zuwa na karbarwa yara na taimako a wajan masu magani?
Malama : Eh za ki iya nemarwa yaranki riga-kafi mana, amma matsalar anan itace: Shin wanne irin magani ne? Kuma wajan wa za kije ki karbo ? Domin a yanzu mata da yawa suna zuwa wajan bokaye wasu basu san babu kyau ba, wasu kuma sun sani, suna karbar kayan shirke-shirke da tsafe-tsafe da sunan .wai
taimako.
Malama taci gaba da cewa: Lallaikam wajibi ne mata su shiga taitayinsu, kuma ku daina zuwa irin wuraren malaman nan ko ince bokayen nan indai har kuna son kwanciyar hankali anan gidan duniya da na lahira, in har ba kwa so ku kwasowa yaranku shedanun Aljanun da zasu hana su zaman lafiya kuma su hana kuma sakat ba.
(Insha ALLAH a rubutu nagaba za muji ci gaban bayanin).
Allah yasa mudace Kuma yakara mana lafiya mai amfani.
Har kullum mu rika tabbatarwa da zuciyar mu cewar: Magani sila ne na waraka amma ba shi da ikon warkarwa, Allah ne kadai mai iya warkar da wanda yaga dama a duk lokacin da yaga dama, shi kadai ne abin dogara ba maganin ba.
(Ayi mana Addu’ar ALLAH ya yarda da mu da ayyukanmu kuma ya lullube mu da RahamarSA.🤲🏻)
Domin karin bayani:
👇👇👇
Domin Ƙarin Bayani Game Da Darrusan Marubucin.
+2348031542026
https://t.me/Rismawymedicine
rismawy86@gmail.com