Alakar Masarautar Kano Da Tijjaniyya

0 1,973

ALAKAR MASARAUTAR KANO DA TIJJANIYA

A lokacin Sarkin Kano Abbas ne wasu malamai na darikar Tijjaniya suka je Kano, kuma sun taimaka wa sarkin sosai da addu’o’i ta yadda zai ci nasara a kan abokan hamayyarsa, musamman wani waziri da aka yi da ake kira ‘Alabar Sarki’, kuma mai karfin fada a ji, wanda har ta kai ya kusan kwace sarautar Kano saboda karfin iko da turawa suka ba shi.

Haka kuma malaman sun taimaka wa Sarkin Kano Abbas wajen samun mafita daga tasirin yakin basasar da aka yi a Kano gabanin zuwa Turawa.

Daya daga cikin manyan malaman na Tijjaniyya shi ne Shariff Ujdud. Mafi yawan masana tarihi na cewa a lokacin sarki Abbas ya karbi darikar ta Tijjaniyya, kuma tun daga wancan lokacin har zuwa yau sarakunan Kano suna bin darikar Tijjaniyya ne.

Gabanin Sarki Abbas dai Sarakunan Kano tun bayan jihadi Suna bin darikar Kadiriyyya ne.
Sai dai kuma wani bangare na masana tarihin masarautar Kano na ganin cewa sai a lokacin Sarki Abdullahi Bayero ne, sarakunan Kano suka fara karbar darikar Tijjaniyya. To amma wannan ra’ayi ba shi da karfi a wajen masana tarihi.

Alakar gidan Sarautar Kano da darikar Tijjaniyya ta kara karfi lokacin da Shariff Alawi ya zo Kano a 1923.

Alakar ta kara karfi lokacin da Sarki Abdullahi Bayero ya hadu da Shaikh Ibrahim Inyass a lokacin aikin hajji, musamman ma saboda ziyarar da Shaikh Inyass ya kai ziyarar farko a Kano a 1945.

tarihin kano

08027270083

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »