Sanadin So (Kashi na 8 Huasa Novel)

0 148

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

SANASIN SO KASHI NA TAKWAS.

KARSHEN LABARI TARE DA BAKIN CIKI DA MAMAKI

Nan danan nahau addu’an daduk tafadomin abakina..tsawon minti 3 nadauka inajiran inji saukan bindigar akaina amma shiru karshen labarin na rufe idanuna ina jiran saukar harsashe a kokonkaina.


Na share akalla mintina uku ina jiran saukar harsashi a kokon kaina. Shirun da na ji ce ta sani bude idanuna. Ganinsa nayi ya ajiye bindigar ya samu wuri ya zauna sai faman huci yake kamar wata kasa.


Ko me ya hanashi harbe kokon kan nawa? Kamar yanda yayi ikirari. Kamar ya san amsar da nake bukata, sai kawai ya fara amsamin. Kaci sa’a, ko kuma in ce Allah Ya yi lokacin mutuwar bai yi ba, shi yasa naji tausayinka.


Wannan shi ne karo na farko da na saita bindigata akan wani mutun, da nufin harbinsa, kuma ban harbeshi ba.


Saboda haka yanzu zan maka Adalci daya. Wancan karon na yi maka hukunci da laifin GANGANCI, alhalin baka yi GANGANCIN ba. TSAUTSAYI ne yasa ka yin laifin, yanzu kuma kayi min GANGANCI, hukuncin ganganci ne ya kamata in zartar a kanka,

amma ba zan yi hakan ba, zan yi maka rangwame, in yima hukunci da wancan laifinka na TSAUTSAYI. Zan karya hannuwan nan naka biyu, wadanda kake amfani da su kana chatin da matan mutane. Sojoji biyu ya kira daga waje ya basu umurnin karya hannuwa duka biyun sannan ya ficewarsa. Ina ji, ina gani suka rika kokowa da hunnuwana kamar masu kokowa da icce har sai da suka kakkaryani, saboda zafin ciwo ban san lokacin da na some ba.

Lokacin da na farka, cikin shagon dinkina na ganni mutane sun kewayeni, bayan sun tambayeni inda ke min ciwo nayi musu bayani wuraren da na karye. Suka kwasheni sai wurin mai dori aka doramin hannuwan nawa sannan suka dawo dani gida domin jinya..

yadda kuka Nayi zaton tunda kwamanda yasa anmun hukunci na karshe shikenan na huta. Ashe akwai abunda yafi hukuncin kwamanda zafi. Kaikanka me karatu dakasha mamakin abunda nagani. Zuciyana ta kone hanjin cikina yakada domin abunda kunnuwa suke jiyemun nayi kukan nadama awannar ranar. Nakwana da mamakin halin mata. Ashe dama haka mace take da sharri?

Nida abokaina ‘yan,uwana munsha mamakin abunda muka gani. Barida nabaku labarin kawai GAYADDA ABUN YAKASANCE Washe gari ina kwance cikin gidanmu, abokina waziri aku ya zo dubina, muna hira. Gefena kuma ‘yar autar dakinmu ne. Hauwa’u jidda. Tayimun girki sosai na kayan cikin saniya. Zaune take tana zubar da hawaye domin tausayin datake gwadawa akaina kasancewar itane kaf dakinmu allah ya hada jinana danata. Samada sauran ‘yan.uwana sai ga sakon fateema ya shigo wayata na ce da waziri aku ya karantamin sakon kasancewar bani da hannuwan rike wayar bare ina karantashi da kaina. Ga sakon kamar haka..

“Gareki Wawiyar zuciya mai cike da kwadayi, ka bani mamaki Kudancy domin kuwa ban zaci zan yi nasara a wannan wasan da sauki haka ba. Na zaci wasan zai yimin wahala ganin cewar da gwani ne zan yi wasar, sai gashi na sami akasin hakan, ashe hangen kitse ne nake yi wa rogo, a yanda nake ganin rubuce-rubucenka na dauka kai gwani ne a wannan wasan ashe wai baka ma san yanda a ke buga wasan ba.

Na san zaka bukaci sanin dalilin buga wasan, to zahirin gaskia lokacin da na fara karo da labaranka, haka kawai na ji na tsaneka, na dade ina nazarin dalilin da yasa na tsaneka, sai daga baya na fahimci ba komai ne ya sa ni tsanarka ba sai ganin cewa kai ba wani marubuci ba,

amma ka dage, wai kai sai kayi rubutu kuma wani abin karin haushi duk rubuce-rubucenka su kan kare ne a wance ta yaudareka, wance ta ci amanarka, wance kuma tayi maka wulakanci, zancen duk daya ne.

Shi yasa na ga ya kamata idan duk wadancan da kake fada sharri ne kake musu, to ni bari in yi maka na gaskiya sai kayi mai dalili Da nayi niyyar kyaleka a dukan farko da mijina yai maka sai kuma naga ai baka doku ba tunda gashi baka daina abinda kake yi a da ba, don haka sai na ga wancan wasan first half ne muka buga ya kamata a ce mun buga second half.

Yanzu kam wasa ya kare tunda nayi nasara. Kar ka manta da ni domin kuwa nima ba zan manta da kai ba. Hawayene ke zuba idon domin jin wannan mummunar sakon na farida nasha mamaki nayi zaton sone na gaskiya ashe cutane dama Tabbas wannan mata ta kai Azzaluma na fada a raina Bata yi kuskure ba da ta kira zuciyata da wawiyar zuciya kuma mai kwadayi, domin kuwa su ne suka bata damar yin nasara a wannan basajar da tayi min wacce ta kira da wasa, sai dai tayi kuskure da ta ce ban san yanda a ke buga wasan ba, domin kuwa ni malamin wannan wasar ne kawai dai idanuna sun rufe saboda kwadayi da kuma wauta, shi yasa na kasa gano bakin zaren wasar, ga shi garin kwadayin nawa na rasa hannuwan da nake rubutun da su, kuma nake dinki ina neman abin sakawa a bakin salati. Karyata ta kare….

Shi yasa da na samu sauki naga ya kamata in zo wa duniyar facebook da wannan labari ko ‘yan uwana samari zasu tsira daga tarkon Basajar matan social network.

WANNAN SHINE KARSHEN LABARIN

Ab Kudancy

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »