Ka San Dalilin Da Yasa Kambun-Baka Da Hassada Ke Shafarka

0 225

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

1- Saboda ka fiye surutu da yawa, duk inda kaje sai ka fadawa kowa abinda kasamu da abinda ka rasa ko abinda kake nema tun kafin ka mallakeshi ba ka da rike sirri.

2- Saboda bakasan illar Kambun-baka bane, domin rabin mutuwar da mutane ke yi a wannan zamanin yawanci Kambun-baka ne sanadi, saboda yana shiga cikin cututtukan zamani kala-kala, suyita wahalar da mutane daga wannan sai wannan. !

3- Wata kila ba ku da sanin cewa akwai masu Kambun-baka a cikin mutane da Aljanu shiyasa kuke ta baza hotunanku da na iyalanku a Social Media ko?

4- Saboda kana Mu’amilantar mutane da taqama da girman kai tare da alfahari kuma Allah ba ya son mai yin alfahari, wanna ma yana iya jawowa mutum Kambun-baka ko hassada su shafe shi.

5- Saboda bakasan cewa: Yin godiya da kuma boye ni’ima tare da yin Addu’a su ne abinda ke sanya Allah ya kiyayeka daga sharrin Kambun-baka da hassada ba.

6- Kun ajiye kuma ba kwayin karatun Alqur’ani da sauraronsa da Azkaar na safiya da maraice da sauran wurare, ai dole kuwa Kambun-baka yayi tasiri a kanku.

Idan har muka kiyaye wannan da ma sauran ire-irensu In Sha ALLAH za mu samu kariya da tsari daga wajan Allah madaukakin sarki mai kowa mai komai.

Allah yasa mudace Kuma yakara mana lafiya mai amfani.

Har kullum mu rika tabbatarwa da zuciyar mu cewar: Magani sila ne na waraka amma ba shi da ikon warkarwa, Allah ne kadai mai iya warkar da wanda yaga dama a duk lokacin da yaga dama, shi kadai ne abin dogara ba maganin ba.

(Ayi mana Addu’ar ALLAH ya yarda da mu da ayyukanmu kuma ya lullube mu da RahamarSA.

🤲🏻

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »