Sarkin Kano Muhammadu Bello Dan Dabo (1882 – 1893) 2

0 536

Nan take Madaki ya juya ya koma gida. Da Sarkin Kano ya ji labari, sai ya kira Sarkin Jahun Modibbo da shi da Sarkin Dutse Bello da Sarkin Kudu na raji da Sarkin Sankara ya umurec su tun da yake ya bayar da umurni an ki bi, to, su tafi Kila gaba dayansu su kai musu harin yaki.

Amma kada su shiga cikin garin, su tsaya a bayan gari, su hana duk mutumin garn walawa. Ba mai fita daga garin,babu kuma mai shiga. Sai su da kansu sun gaji sun bi umurnin Sarki.

To, sufa mutanen kila garinsu ne, Jarumawa ne sun san hanyoyln Shiga da fita. Haka kuwa akayi kawai akaga sun fita suna ta yankan baya, suna harbin masu tsare da su, An Sami kwanaki arbain a kan haka. Sai sarakunan nan suka aika wa Sarkin Kano halin da ake ciki, amma Sarki bai ba su izinin su fadawa garin da yaki ba.

Da Suka ga sun sanar har sau uku ba a ba su izinin su fada wa garin da yaki ba sai suka fara tsammanin ko Sarki so yake yi a kare musu mutanensu. Ba su yi tunanin Sarki Bello ba ya son yaki ba, don kada a zubar da jini.

Daga nan suka yanke shawara kowa ya koma gida wato ke nan sun yi Wa Sarkin Kano Bello tawaye.

Yayin da Sarkin Kano Bello ya ji yadda sarakunan nasa sukayi masa bore, Sunki bin umurninsa sosai sun ki tsayawa, sai ya tayar da mutum, ya aike shi zuwa ga Sarkin Gaya Garba mai joni Joni aka Kirawo shi. Sarkin Kano Bello ya fada masa dukkan abin da sarakunan nan hudu suka yi masa.

Sai ya umurci Sarkin Gaya da shi ma ya tafi kila inda wadan can suka baro, amma shi ma kada ya shiga garin da yaki, Saboda Da baya so a zubar da jini, sai dai ya hana dukkan mutan garin shiga da fita, Kada kowa ma ya wala. Idan su da kansu sun matsu sun tsoruta, sun bi umurnin Sarki, sannan ya dawo.

To, shi Sarkin Gaya a wannan Zamani ya fi wadancan sarakunan kasaita da Karfi, haka zalika shiryayye ne, Jarumi kuma a fagen daga kowa ma yana tsoran sa, ana shakkar sa saboda yawan kayan fada. Dawaki kadai da ‘yan kasa yana da fiye da dubu biyu, tukuba da masu da majajjawa da sango da kibau da asigiri da garkuwa da sulke da kwalkwali sun fi a kirga.

Yayin da aka ga Sarkin gaya ya isa Kila tare da wadannan kayan fada, duk sai mutanen Kila suka firgita suka dimauta kowa hankalinsa ya táshi Saboda tsoro. Gani ake yi dare daya tak zai lya gamawa da su, ya cinye garin. Amma ina! Sarki bai bayar da umarni ba.Sarkin Gaya ya zurce Zandam ya yi zamansa, yana ta ba su tsoro.

Kullum daren Allah sai ya yi ta kwarara bindiga kamar gaske, amma ba abin da ya faru. Sarkin gaya ya zauna har tsawon wata uku har aka fara yi masa dariya, ana cewa ya kasa cin Kila, da yaki ya yi dariya ya ce ni ai izinin Sarki kawai nake jira. Amma in har sarki zaice a kamo Yan garin ai dukka zan iya kamowa da hannu.

Kai a takaice dai sau uku Sarkin Gaya yana aikawa SarKin Kano Bello ya ba shi izini ya yaki Kila Amma Sarki yana ki Saboda haka ba tare da izinin Sarki ba, daya ga mutanan sa na raguwa saiya koma gida, daga Nan yayi watsi da umarnin Sarki, Kuma yaki Zuwa Kano a lokacin da Sarki ya umarci yazo yayi Masa bayani harma wani makadin sarkin Gaya yake cewa:

ldan da mai fada, ya fada,
Garba ba Za ya zoba


Ya ci da Karfi,
Ya kwace Gaya.


Ya huce haushi
Ya gwada karfi.

Amma daga bisani Sarkin Gaya ya zo Kano ya y tuba ga Sarki aka yafe masa.

Sarkin Kano Muhanmmadu Bello ya yi sarauta har ta tsawon shekaru goma sha daya da wata bakwai, sannan ya rasu a gidansa na Kano, aka binne shi a shekar yamma ta gidan Sarki. Daga nan aka aika wa Sarkin Musulmi da dokinsa da takobinsa don ya shaida,

kuma a wannan lokacin ma Wazirin Sakkwato yana Kano domin wata zyara. Allah ya jikan Sarki Muhanmmadu Bello, ya sanya aljanna makomarsa, amin.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »