Tuwan rogo (fufu, ko kuma abo) tuwo wanda yake kamar tuwan semo, sai dai yanada dan banbanci wanjen sarfashi.
Fufu yanada dadin ci sosai musan man a hadashi da nau’in miyar da take da yauki kamar kubewa da sauransu. Wannan rubutu zai kawo muku hanya mafi sauki da zakuyi tuwan ABO.
Da farko uwar gida zata samu rogon ta masu kyauta saita feraye bawon jinkin rogon, sai ku yayanka shi zuwan yan kanana-kanana, idan kun gama saiku wankeshi da ruwa maikyau.
Bayan kun wanke sai ku samu mazubi kuzubashi a ciki ku kawo ruwa mai kyau ku zuba masa har yasha kansa. Zaku barshi a cikin wannan ruwa har na tsawon kwana daya (1).
Bayan ya kwana sai a debeshi daga cikin ruwan, zakuji yayi laushi sosai sai ku kuma wankeshi da ruwa mai kyau. Sai ku sami abin nikawa ko markadawa kamar Blender ko kuma wani abu daya fimuku sauki sai ku markadashi.
Bayan kun gama markadashi sai ku samu abin matsewa, kamar wanda ake matse gasarar koko. Sai ku zubashi a ciki ku daure bakinsa, ku kawo wani abu mai nauyi ku dora a kansa yadda ruwan zai matse sosai ba tare da ya rage wani ruwa a jikinsa ba. Zaku barshi har tsawon awa 3 zuwa 4 yadda ruwan zai fita baki daya sai dusar rogon.
Sai ku dauko tunkunya ku dora akan wuta, ku zuba ruwa daidai, sai ku dauko wannan dusar rogon da kuka matsae ruwansa kuzuba a ciki kuna juyawa saboda kada ya dunkule.
Zakuyi ta juyawa kamar dai yadda kuke juya rudan tuwa, har sai yayi kamar tuwa, saiku kawo ruwa ku zuba a ciki ku rufe yadda zai dahu sosai kamar tuwo. Bayan ya daho sai ku sauke ku kula a leda kamar yadda kike saka semo.
Shikenan tuwan FUFU ko ABO yayi sai ci. Zaku iya cinsa da kowace miya da kuke so.
Kuna da damar kuyi tambaya idan akwai step daya shige muku duhu. idan kuma kun gane to kuyi share please.