Bani Da Lafiya Kashi Na Tamanin Da Takwas (88) Addu’oin Da Ya Kamata A Karantawa Yara.

0 542

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Malama taci gaba da cewa: Kuma Annabi Sallallahu alaihi Wasallama ya koyar da mu Addu’o’in da za mu rika karantawa tare da iyalanmu domin nema da samun kariyar ALLAH daga dukkanin sharrin halittunSA.

Kuma ya hana mu karbar duk wani maganin neman tsari da kariya wanda yasabawa Tafarkinsa Saboda tafarki biyu ne a duniya matukar kabar tafarkin Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama to sai kuma tafarkin Shedan ( La’anannen Allah), ALLAH yakara tsare mana imaninmu.

Daga cikin Addu’o’in da suka fito daga fadar Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama su ne kamar haka:

(1)-
أعوذ بكلمات الله التامات من غضبه وعقابه ومن شر عباده ومن همزات الشياطين وأن يحضرون.

“A’UZU BIKALIMATILLAHI ATTAAMMAH MIN GADHBIHI WA IQAABIHI WA MIN SHARRI IBADIHI WA MIN HAMAZAATISH SHAYAATEEN WA AN YAHDURUN.” (Safe da yamma).

(2)-
أعوذ بكلمات الله التامة من كل شيطان وهامة ومن كل عين لامة

“A’UZU BIKALIMATILLAHI ATTAAMMAH MIN KULLI SHAITAANIN WA HAAMMAH WA MIN KULLI AININ LAAMMAH.” (Safe da yamma sau 3)

(3)-
أعوذ بكلمات الله التامات من شر ما خلق.

‘A’UZU BIKALIMATILLAHI ATTAAMMAAT MIN SHARRI MAA KHALAQA.” (Safe da yamma sau 3).

Wadannan da kuma Ayatul Kursiyyu, Suratul Ikhlas, Suratul Falaqi da Suratul Nasi duk ana so ne a koyawa yara su har su iya karanta su kuma su haddace su, idan kuma basu fara magana ba ko bazasu iya karantawa ba sai a rika tofawa a tafin hannuwa ana shafe musu jiki da shi.

Kuma ita lamba ta (1) ana karantawa yaro ita ne hatta idan yana yawan kukan dare mara dalili, ko yana firgita ko zabura cikin dare ko rana, sai a rika dafe masa jikinsa (kirji ko ciki ko kansa) ana karanta ta ana tofawa. In sha ALLAHu akwak mai fa’idah a wannan kuma yaro zai samu sa’idah.

(In Sha Allah a rubutu nagaba za muji ci gaban lamarin.)

Allah yasa mudace Kuma yakara mana lafiya mai amfani.

Har kullum mu rika tabbatarwa da zuciyar mu cewar: Magani sila ne na waraka amma ba shi da ikon warkarwa, Allah ne kadai mai iya warkar da wanda yaga dama a duk lokacin da yaga dama, shi kadai ne abin dogara ba maganin ba.

(Ayi mana Addu’ar ALLAH ya yarda da mu da ayyukanmu kuma ya lullube mu da RahamarSA.🤲🏻)

Domin karin bayani:
👇👇👇

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »