Abubuwan Da Ya Kamata Ku Sani Game Da Dabbar Bodari.

0 260

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Kalamar BODARI da Hausa ne amma da yaren ingilishi ana kiransa da suna Polecat Afrika ko kuma kace zoril, zorille, zorilla, Cape polecat, ko kuma Skunk na Afirka wannan duk ana iya kiransa dashi.

Tsayin sa ya kai santimita 60-70 Wanda yay dai dai da inci 24-28, daga Kansa zuwa Jelar sa. Sannan iya jelar sa tana da tsayin 10-15 santimita, haka zalika suna da nauyin da yakai 1.3 kilo gram bakake ne, amma akwai farare masu ratsin fari da baki, su na rayuwa tsawon watanni 160.

Saboda yanayin rayuwar sa da yawan mutane basu taba ganin wannan dabbar ba, amma sunanta ya shahara. Akwai sama da jinsi goma na wannan dabba dake rayuwa a duniya. Su na cin abinci da yawa daga dangin kwari, nama, da ‘ya’yan itatuwa, Kwai da mushe. Saboda basu jin dafin maciji, su na cinsa da yawa kuma suna son zuma sosai yasa suke ziyarta inda ta ke.

Duk wanda yasan tarihin kasar Hausa yasan cewa ana danganta wannan dabba da tusa amma ba haka abin yake ba. Dangin dabbobi irin su Zaki da Damisa suna yin fitsari na wani sinadari dake nuna cewa nan wajen mallakar su ne, territory marking a turance. Kamar yanayin haka, shi Bodari yana fitsarin sinadarin sulphur ne lokacin da ya fuskanci barazana daga abokan gaba domin kare kansa. Wannan sinadarin shi ne mai matsanancin wari wanda ana iya jinsa har fiye da tsawon kilomita biyar.

Wannan sinadarin yana da kaikayi, radadi, kuma yana haddasa makanta ta dan wani lokaci haka ma yasa ko manyan dabbobi a dawa suke bashi girma idan sunyi gamo don zaman lafiya.

Bodari dabba ce mai son yawo da dare ko sassafe, ko lokacin da duhu ya fara shiga, amma da zarar gari ya waye sosai sai kuma ya kwanta yayi ta bacci har zuwa duhu ya fara.

Yana da matukar karfin hanci, amma baya gani sosai. Idan kai ma’abocin tafiya ne da safe watakila ka taba ganin mushensa mota ta take shi saboda rashin ganin sa sosai.

Lokacin kiwo yawanci sunayi ne a cikin bazara, kuma matansu suna haihuwar Ya’ya 2 zuwa 5.

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »