Allah Maɗaukakin Sarki Yan faɗa a Alkur’ani cewa:
وَيَسْتَلُونَكَ عَن ذِي الْقَرْنَيْنِ قُلْ سَأَتْلُوا عَلَيْكُم مِّنْهُ ذِكْرًا • إِنَّا مَكَّنَّا لَهُ فِي الْأَرْضِ وَءَاتَيْنَاهُ مِن كُلِّ شَيْءٍ سَبَبًا • فَأَتْبَعَ سَبَبًا
Suna kuma tambayar ka game da Zulkarnaini; ka ce (da su): “Ba da dadewa ba zan ba ku labari a kansa.” Lalle Mu Muka kafa shi a bayan kasa, Muka kuma ba shi hanyar cimma duk wani muradinsa.
Sai ya bi hanya.
An tambayi Sayyidina Aliyyu (Allah ya kara masa yarda) cewa,: Shin Zul-Karnaini annabi ne? Sai ya ce: “Ya kasance bawa ne na kwarai, ya so Allah sai shi ma Allah ya so shi, ya yi nasiha don Allah sai shi ma Allah ya yi masa nasiha, sai ya tura shi wajen mutanensa, suka yi masa duka guda biyu a kansa, don haka ne ake kiran sa Zul-Karnaini….” [Ibnu Jarir, Juzu’i na 16, shafi na 16].
Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, ya ba shi mulki mai karfi a bayan kasa, don haka ya riki duk wani abu da Allah ya hore masa ya kama hanya don cimma burinsa.
Zul-karnaini dai wani Sarki ne mumini mai Kadaita Allah, wanda ya yi imani da ranar lahira. Allah ya ba shi karfin mulki har ya ci garuruwa masu yawa da yaki. Allah kuma ya ba shi duk wani abu da mai mulki a zamaninsa yake bukata don wanzuwar mulkinsa da tabbatar da adalci a bayan kasa. Ya kasance mai kira ne zuwa ga Allah, da yaki da duk wani mai bautar wani ba Allah ba. Zul-Karnaini ya kewaye duniya da yawo, ya isa yammacin duniya, daga nan ya dawo ya danna gabashinta inda ya isa wurin da ya gina babbar ganuwa tsakanin kabilun Yajuju da Majuju da sauran makotansu. Yana karbar umarni ne ta hanyar wahayi da ake yi masa kai-tsaye (idan shi annabi ne), ko ta hanyar wani annabi da ke tare da shi a cikin rundunarsa.
Zul-Karnaini ya ci gaba da tafiya a bayan kasa da rundunarsa, har ya isa karshen kasa ta nahiyar yamma inda dan adam a lokacin ba zai wuce shi ba. Kuma nan ne mafadar rana, ya gan ta tana faduwa cikin wani marmaro wanda yake cakude da tabo mai launin baki mai wari. A nan ne ya ga wasu mutane kafirai wadanda suke bautar gumaka ba Allah ba, suna rayuwa kamar dabbobi ba addini. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ba wa Zul-Karnaini zabi cewa, ko dai ya azabtar da mutanen nan ta hanyar kisa ko waninsa idan sun ki yin imani, ko kuma ya bi su ta lalama da kyautatawa.
Sai Zul-Karnaini ya bayyana cewa, duk wanda ya yi shirka da Allah ya doge a kan kafirci bayan an yi masa wa’azi an nuna masa gaskiya, to zai yi masa azaba a nan duniya ta hanyar kisa, sannan ya koma ga Ubangijinsa ranar alkiyama ya yi masa mummunar azaba.
Ya kuma bayyana cewa, daga cikinsu duk wanda ya yi imani da Allah ya yi kyakkyawan aiki, to yana da sakamakon gidan Aljanna, sannan zai fada masa tattausar magana daga lamarinsa.
Sai kuma Zul-Karnaini ya ci gaba da tafiyarsa da sojojinsa bayan ya gama tabbatar da umarnin Allah a kan wadannan mutanen.
Zul-Karnaini ya ci gaba da tafiyarsa a bayan kasa inda ya dawo kuma ya nufi nahiyar yamma, watau mahudar rana. Ya kuma sami rana tana fitowa a kan wasu mutane wadanda ba su da wata kariya da za ta kare su daga zafin rana, domin ba su da gidaje kuma inda suke babu bishiyoyi da za su fake a inuwoyinsu, domin a kasarsu babu dutse babu bishiya, kuma kasar ba za ta dauki gine-gine ba.
Al-Hasanul Basri ya ce: “Kasarsu ta kasance ba ta daukar gini a kanta, sun zamanto duk sa’adda rana ta fito musu sai su gudu su shiga cikin ruwa, idan ta fadi sai su fito su ci gaba da kiwo a waje kamar dabbobi.” Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, rayuwar wadannan mutanen irin rayuwar mutanen nan ne da Zul-Karnaini ya samu a mafadar rana, su ma kafirai ne kuma masu aikata laifuffuka da barna a bayan kasa. Don haka su ma ya tafiyar da lamarinsu kamar yadda ya yi tare da wadancan mutanen na farko.
Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya nuna yana sane da halayen da Zul-Karnaini yake ciki shi da rundunarsa, yana kuma yi musu jagora.
Zul-Karnaini ya ci gaba da tafiyarsa tare da sojojinsa har ya kai ga wata hanya tsakanin wasu duwatsu biyu, a kusa da su kuma ya sami wasu mutane wadanda ba sa fahimtar wani yaren da ba nasu ba. Da suka fahimci cewa, Zul-Karnaini Sarki ne adali sai suka kai masa kukansu na wasu kabilu biyu da ake kira Yajuju da Majuju, suka shaida masa cewa, su wadannan kabilu mabarnata ne a bayan kasa, suna kawo wa sauran kabilun yankin hare-hare, suna kashe na kashewa su wawashe wa jama’ar gari dukiyoyinsu su lalata musu gonakinsu.
Yajuju da Majuju dai suna daga cikin zurriyyar Annabi Adamu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi). Kamannin halittarsu irin ta sauran ‘yan’adam ce babu wani bambanci, suna da yawan gaske da yawan barna da ta’adi a bayan kasa. Hakan ya sa kabilun suka nemi Zul-Karnaini da ya taimaka musu wajen magance yawan hare-hare da suke kawo musu. Suka tambaye shi cewa, ko zai yarda su ba shi wani lada don ya sanya wani shamaki tsakaninsu da su? Sai Zul-Karnaini ya amsa musu da cewa, abin da Allah ya ba shi na karfin mulki ya fi duk wani abu da za su tara masa, taimakon da kawai yake nema a wajensu shi ne na ma’aikata da kayan aiki na gini da sauran abin da aikin gina ganuwar zai bukata, shi kuma zai gina musu wannan shamaki a tsakaninsu.
Ya umarce su da su kawo masa guntattakin karafa manya-manya, suka kuwa kawo masa, nan take ya fara gina ganuwa tsakanin wadannan duwatsu guda biyu, har ginin ya kai daidai tsawonsu, sai ya umarci ma’aikatansa da su kunna wa guntattakin karafan nan wuta har sai da suka yi ja jawur, sai ya umarce su su kawo masa narkakkiyar dalma don ya zuba ta a kai. Bayan haka da ta huce ta daskare sai ta zama wani curarren abu guda mai matsanancin karfi wanda ya zama ganuwa tsakanin Yajuju da Majuju da sauran kabilu mazauna wannan wuri.
Allah ya bayyana cewa, tun bayan gina wannan ganuwa Yajuju da Majuju ba su sami ikon haura ta ba da dawakansu da makamansu domin kai hare-hare, kamar yadda suka saba a baya, haka kuma ba su sami ikon huda ta ta kasa da digoginsu ba.
An karbo daga Zainab ‘Yar Jahshin )رضي الله عنها ce: Wata rana Annabi () ya shigo mata a firgice yana cewa,: “La Ilaha Illallahu, Larabawa sun banu daga wani sharri da ya kusanto! A yau an bude wata ‘yar kofa daga ganuwar Yajuju da Majuju kamar haka.” Sai ya hada babban dan yatsansa na hannu da mai bi masa ya yi kawanya da su. Sai Zainab ta ce:
“Ya Manzon Allah, yanzu za a halaka mu alhalin a cikinmu akwai mutanen kirki?” Sai ya ce: “Na’am, idan na banza suka yi yawa.” [Bukhari #3346 da Muslim #2880].
Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ci gaba da bayyana cewa,, yayin da Zul-Karnaini ya dubi aikin wannan ganuwa ya ga ya kammala kamar yadda ya tsara, sai ya bayyana cewa, wannan rahamar Ubangijinsa ce ga mutane da ya tausaya musu, don haka ya tsare su daga sharrin Yajuju da Majuju da wannan ganuwar. To amma fa duk lokacin da wa’adin da Allah ya ajiye na fitowarsu ya zo, watau gabanin tashin alkiyama, to zai baje wannan ganuwar ya mayar da ita daidai da kasa kamar ba a taba gina wani abu a wurin ba, kuma tabbas alkawarin Allah gaskiya ne sai ya tabbata.
A wadannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, zai bar mutane a wannan ranar suna cakuda da junansu. Wannan aya ta 99 za ta iya daukar ma’anar cewa, ranar da Allah (Mai tsarki da daukaka) zai kaddara fitowar Yajuju da Majuju bayan ganuwar nan ta fashe, za su fito da yawa suna gauraya da mutane, suna ta barna a kan dukiyoyinsu da lalata musu kayansu. Wannan kuwa zai faru ne kafin tashin alkiyama.
Allah Ya sa mu cika da imani.
Daga shafin Bashir Halilu.