TARIHIN SARKIN KANO ALU BABBA KASHI NA 2

0 1,586
WANNAN SHINE CIGABAN TARIHIN SARKIN KANO ALU

Bayan Sarki Aliyu ya Gama ziyarar sa gami da shawarwari da Sarkin Musulmi, yabashi, ya baro Sakkwato ya nufo Kano zai dawo gida.

Suna kan hanyar dawowa gida sai ga wani yaron Sarkin Shanu ya ba shi labarin cewa ranar Talata 4 ga watan Zulkida turawa sunci Kano da yaki sun kashe Sarkin Shanu Dangwari a gidan Sarki.

Sun kashe Sarkin Bebeji Malam Jibrin a gidansa dake Bebeji, daga baya Kuma Sai Sallama yazo yace sunci Kano da yaki sun shiga gari, iyalan Sarki wasu an kaisu Gogel wasu Kuma suna wasai wayannan Kuma mun iso tare dasu.

Sarkin Kano Aliyu ya juya akalarsa sai Birnin Goga nan ya zauna daga nan Sarki ya yi niyya ya tafi inda suka yi aikawari da su Sarkin Musulmi don su tafi neman taimako a Kan Turawa batare da wani ya sani ba. A kan hanyar Sarki Aliyu ne ya yi zango a birnin Kwanni.

Sarkin Kano Aliyu yana birnin Kwanni ne, Magajin Kwanni ya aika wa turawa, su zo maza-maza ga Sarkin Kano Aliyu a kasarsa. Turawa Suka tarar da Sarki, suka dauki botonsa a kofar masaukinsa kusa da wani babban daki.

Tun a wannan lokacin ne Suka fara tafiya da Sarki da nufin zawu kai shi kasar Adamawa.

Kwanci tashi kullum suna tafiya, wata rana da suka farka basu ga Sarki ba, sai Suka yi duru-duru, su duba nan su duba Can, ashe Sarki ya tafi kama ruwa.

Daya fito Sai Sojojin Nan sukayi kansa, shikuwa Sai yace musu ai baku kuke tsare dani ba kaddarar Allah ce wadda tuni na yarda da ita Amma dabadan haka ba da tuni na gudu bazaku sameni ba. Amma a hankali zan gwada muku, Sai Soja suku kyale shi.

Kashegari kuwa dukkan sojojin da suke tsare da Sarki da dare ya yi sai suka fara barci har zuwa hantsi babu wanda ya tashi daga barci. Sai Sarki ya debe dukkan bindigoginsu ya kai su wani kogon kuka ya boye su, ba su farka daga barcin ba, sai da rana tsaka. Suna farkawa sai suka ga babu bindigoginsu, Sa suka yiwo kan Sarki suka rirrike shi, ya ce ku sake ni, tuni na gaya muku ba ku kuke tsare dani ba, ikon Allah ne, kun ga wata kuka can, ku je ku duba, ku dako bindigoginku a cikin kogonta.

To daga nan ne suka daina tsananta wa Sarki har suka iso Adamawa Kasar Yola, aka kai Sarki masauki a wata unguwa inda Hausawa Suke da zama, ana kiran ta da suna wuro Hausa. A nan suka zaunar da Sarki har sai da ya shekara kamar biyu.

A can garin Wuro Hausa Kuwa Duk ranar Juma’a kuwa idan Sarki ya dawo daga masallaci duk jama’ar kasar da wasu na garin sai sukan biyo shi har gida kamar dai a kasarsa yake. Tsoron wannan al’amari na nuna goyon bayan mutane ga Sarki, sai Turawa suka rika zaton a nan ma Sarki zai iya afka musu da fada.

Ganin haka sai suka dauke shi daga Yola suka kai shi Lakwaja, a inda ya tarar da wasu sarakunan da aka ci kasarsu da yaki. Su ma an kai su can an zaunar da su.

Irin su Sarkin Bida Abubakar da Sarkin Musulmi Tambari da Sarkin Zazzau Alu dan Sidi.

A can Sarki Aliyu ya yi zamansa lafiya, ba ya fitowa balle yaje gidan kowa, sai ma wata rana da ya fito da asuba ya ce a kai shi gidan Sarkin Zazzau, mutane suke ta mamaki. Da ya isa inda yake sai ya tarar da shi tuni rai ya yi halisa, jama’a ba su sani ba, sun dai san Sarkin Zazzau ba shi da lafiya, a sannan ya sanar da mutanen gidansa cewa Sarkin Zazzau Alu dan Sidi ya rasu.

Sarkin Kano Aliyu ya rasu ne a Lakwaja kuma a nan ne aka binne shi. Allah ya gafarta masa amin.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »