HAUSAWA DA SADARWAR INTANET

0 238

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

INTANET DA BAZUWARTA A QASAR HAUSA

Kusan a yau intanet ta game dukkan jihohin da ke arewacin Nijeriya, domin aqalla ba a rasa mashaqatar Tsallake-Tsallake a kowane babban birnin qasar Hausa. (Adamu, 2004:8). Alummar Hausawa na samun damar shiga intanet ne ta hanyoyi guda uku kamar haka:

  • Hanya ta farko, ita ce ofisoshi, saboda samuwar kwamfutoci a Jamioi da Ofisoshi da Asibitoci, zuwa dakunan karatu. Wadanda aka hada da layukan intanet.
  • Hanya ta biyu ita ce mallakar kwamfutar tare da hada ta da layin intanet, ga manyan maaikatan gwamnati da masu hannu da shuni a garuruwan Hausawa wadda suke amfani da ita ko kuma yayansu.
  • Hanya ta uku kuwa, ita ce ta mashaqatar Tsallake-Tsallake (Cyber Café). A da hukumar wannan sadarwa ta qasa ce kawai take da ikon hada mutane da wannan fasaha, amma daga baya, an samu kamfanoni da ke hada kwamfutocin da intanet ta hanyar tauraron dan adam (Broad-band). Don haka, masu shaawa sukan je su biya kudi daga mintuna talatin zuwa sama, domin yin bincike a giza-gizan sadarwa na intanet.

Babu shakka, a bayyane yake cewa, a yanzu ne intanet ta fara yaduwa a qasar Hausa, amma ta hanyar wayar da kan mutane dangane da muhimmancin wannan fasaha, to yawan masu amfani da ita zai qaru.

YADUWAR ALADUN HAUSAWA A INTANET

Kusan tun shekaru goma kafin isowar intanet qasar Hausa, bayanai cikin harshen Hausa suka fara hawa giza-gizan sadarwa na duniya. Duk da cewa shafukan sadarwa na intanet masu dauke da bayanan da suka shafi Hausawa da adabinsu cikin Turanci suke, a yanzu ana samun na harshen Hausa wadanda suke dauke da bayanai cikin Hausa.


Yawancin masu wannan qoqari na yada adabi da aladun Hausawa a intanet yan asalin Nijeriya ne, wadanda suke zaune a qasashen waje, da kuma wasu mazauna Nijeriya, sai kuma Turawa yan qasashe daban-daban masu shaawar bincike a kan harshe da aladu da kuma adabin Hausawa.

Wasu daga cikin wadannan shafuka da za a iya samun bayanai masu tarin yawa kan wadannan fannoni sun hada da:

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »