Rubutattun Kalmomin Hausa Masu Ma’ana Sama Da Ɗaya

0 447

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

A harshen Hausa, akwai kalmar da a rubuce ta kan ba da wata ma’ana, to amma a magana za ta iya haifar da wata ma’anar daban, ko ma fiye da ɗaya. Irin waɗannan kalmomin, wajen rubuta su ba a ƙara masu wasali ko wani ɗigo ko wata alama. Sai an saka su cikin jimillar zance ne ake gane inda ake so su dosa. Wani abu da na gano game da irin waɗannan kalmomin shi ne duk guntaye ne, sannan na biyu kuma yawancin duk wata kalma da aka aro ta daga Larabci ko Turanci ba ta bayar da ma’ana sama da ɗaya (misali sadaka, waliyyi, alfijir, malami, table, basukur, fanka, rediyo, janareto, da sauran su).

Ga misalan kalmomin da a rubuce za su iya ba da ma’ana sama da ɗaya, kuma na fassara su da Turanci don a fi saurin ganewa:

baba (father, mother, dye)

bori (spirit worship, bad groundnut, go haywire)

ci (eat, lovemaking)

ciwo (wound, a wild fruit)

daga (from, struggle)

dama (right side, mix)

dawa (forest, sorghum)

dara (world, a game, a cap)

doka (law, beat, a tree)

doki (beat, horse)

fafa (cut a calabash, boastful)

fata (skin, hope)

fito (whistling, come out, assistance in crossing a river)

gaba (front, enmity, private part)

gaɓa (joint, river bank)

gado (inheritance, bed, a bird’s name)

gara (it’s better, silly person, termite)

gari (flour, town)

giɓi (space, gap between teeth)

gora (gourd, heavy stick)

gyaɗa (groundnut, nod head)

iya (able, mother)

ja (red, pull)

kada (don’t, crocodile)

kaɗa (drum beating, cotton, push)

kai (you, head, take it there, exclamation of surprise)

ƙaura (migration, type of sorghum, armed hunter, warrior)

ƙauye (village, aside)

mace (female, dead)

mai (oil, of)

mama (mother, breast, take by surprise)

mara (food measurement, pubis, slap, lacking in something)

mata (wife, women)

matashi (young man, pillow)

rana (sun, date)

ruga (run, Fulani settlement)

sabo (new, familiarity)

sarki (emir, group head)

sauna (fool, fear)

saura (remains, empty farm in dry season)

sheƙa (downpour, bird’s nest)

suma (fainting, hair on head)

sura (chapter, portrait)

wawa (fool, grab)

yari (chief prison warden, cloth decoration)

yarinya (small girl, girlfriend)

yaro (small boy, son, staff)

zagi (insult, escort)

zana (draw a picture, thatch wall)

zobe (ring, encircle)

zuga (instigate, blow fire)

Ko za ku iya tuno da ire-iren waɗannan kalmomin?

Rubuta wa: Ibrahim Sheme

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »