HAUSAWA DA SADARWAR INTANET

0 238

A taqaice dai wannan tsari ne wanda ta hanyar habakar fasahar sadarwa ta kwamfuta, cikin yan daqiqoqi ana iya hada babbar hulda tsakanin qasashe masu nisa a kowane yanki na duniya.

Yanzu sai ka iya gani kuma ka ji abin da yake aukuwa a nisan duniya, alhali kai kana zaune ko motsawa ba ka yi ba. Kuma yanzu sai mutum ya iya jiyo dimbin bayanai game da kusan kowane fanni na ilimi da ake da shi a duniya, wanda idan ba haka ba, adana shi sai a babban ginin Laburare.

(Muhammad, 2004:5). Leiner da wasu (2003:2) sun nuna cewa fasahar sadarwa ta intanet ta samo asali ne tun wajejen 1958, a lokacin da Tarayyar Rasha ta qaddamar da fasahar sadarwa mai suna SPUTNIK.

Wannan shirin na Rasha, shi ya zaburar da Amirka, har ta samar da cibiyar gudanar da zuzzurfan bincike mai suna ARPA.

Wannan cibiya ce ta samar da ofishin fasahar sarrafa bayanai qarqashin jagorancin J.C.R Linklider da taimakon Lawrence Roberts suka gudanar da aikin harhada kwamfutoci domin musayar bayanai.


Baya ga haka, sashen kula da ayyukan tsaro na Amirka ya yi shirin hada garuruwa da sadarwar intanet domin adana bayanai, ko da za a lalata wani sashe na bayanan sakamakon yaqi ko wata annoba, sai su yi qoqarin fitar da shi a wani garin.

Daga baya manyan makarantu da masu binciken kimiyya da hukumomi,sun sami damar yin amfani da wannan fasaha domin bincike da kuma sadarwa.

A wajejen 1992 ne gwamnatin Amirka ta janye hannunta daga kulawa da tafiyar da wannan fasaha, wanda tun daga wannan lokaci ne yan kasuwa suka sami damar yada ta domin amfanin jamaa. Kuma wannan dalili ne ya sa ta ci gaba da yaduwa har zuwa yau.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »