Hausawa al’umma ce da ke zaune a Arewacin Nijeriya da wani yanki na Nijer da Chadi, waɗannan jama’a sun kasance mutane ne masu al’adu da ɗabi’unsu na asali wanda ya sa cakuɗa da sauran al’ummomi kamar Labarawa da Turawa ya yi tasiri game da al’adun nasu.
A Bahaushiyar al’ada namiji ke jagorancin gida, aikin mace kuma ya haɗa da:
a) Rainon yara
b) Dafa abinci da kuma
c) Kula da gida.
A zamanin da mace ba ta da daraja sosai a gurin Bahaushe domin sai yadda maigida ya yi da ita, ba za ta je makaranta ko aiki ba, bare uwa uba ta yi siyasa. Bayan zuwan addinin Musulunci da Turawa sai wannan al’amari ya sauya. (Azima, 2007).
Bahaushe kafin zuwan Musulunci yana da damar auren mata ko guda nawa ya ga zai iya ba tare da ƙayyadewa ba. Wannan ya dogara ne da halin da yake da shi. A wurin su auren mata da yawa wata hanya ce da mutum zai ƙara tattalin arziƙinsa. Domin babbar sana’ar Hausawa a wannan lokaci ita ce noma, idan kuma an tashi noman tare ake yi da mata. Wato wanda yake da mata da yawa gonakin da zai noma suna da yawa ke nan, don haka amfanin gonarsa ma zai yi yawa.
Bayan zuwan Musulunci sai ya zamana Bahaushe ba shi da ikon ya auri mace fiye da huɗu, kai in har ba zai yi adalci ba, bai kamata ya auri fiye da ɗaya ba ma.
Matan Hausawa sun saba zama da kishiya, don haka idan namiji ya auri mace fiye da ɗaya sai su yi zamansu tare a gidan mijin. To da yake yau da gobe sai Allah, wannan zama da suke tare kan sa a sami rashin jituwa a tsakaninsu, saboda kishi wanda ke haifar da yin habaici a tsakaninsu domin cimma wani buri na rayuwarsu.
Bincike ya nuna asalin kalmar habaici ba za a iya danganta ta da wani harshe ko wata ƙabila ba, ban da Hausa. Ma’ana an sami kalmar habaici daga harshen Hausa ba tare da an aro ta daga wata ƙabila ko wani harshe ba.
Wannan ya tabbatar da Bahaushiyar kalma ce wadda ba za a iya cewa ga lokacin da aka fara amfani da ita ba. Habaici yana daga cikin maganganun hikima da nuna gwaninta da naƙaltar harshe da Hausawa suka gada iyaye da kakanni.
Hausawa sun taso suna shirya habaicinsu da ka ne a cikin maganganunsu na yau da kullum ko a cikin waƙoƙi, sannan su adana abinsu da ka. Habaici yakan sami ci gaba dangane da juyawar lokaci ko zamani.
Bincike ya nuna a harshen Hausa ita kalmar habaici an gina ta ne daga abin da aka yi shi bayan wani abu ya faru. Ka ga a nan “ɗan baicinka” na nufin ɗan bayanka ke nan. Haka kuma idan an ce “ni da kai muka yi maganar baicin ya san an je an yi alƙawari da shi a kan abubuwan. Wannan kalmar baicin tana nufin bayan wani abu ya faru ke nan.
Haƙiƙa yanzu ba za a iya cewa ga zamanin da al’ummar Hausawa suka fara yin amfani da habaici a cikin maganganunsu ko rayuwar su ba. To amma an samu Hausawa suna yin habaicin tun daɗewa, haka kowa ya taso ya tarar Hausawa suna shiryawa da ka kuma suna faɗar abin su da baki a cikin waƙoƙi ko a cikin maganganunsu.
Haka kuma ma’anar habaici ba ta canzawa, sai dai ana samun sababbin habaici dangane da ci gaban al’ummar wajen ƙere-ƙeren da harshen ke yi na sarrafa harshen ko kuma saboda yanayin wannan zamanin da ake ciki.
Habaici abu ne mai matsayi ga al’ummar Hausawa kamar yadda sauran kashe-kashen adabin baka ke da matsayi, don shi ma ya ƙunshi hikimomi na sadarwa tsakanin al’ummar.
Habaici abu ne wanda al’ummar Hausawa suke amfani da shi yau da kullum wajen zantuttukansu. Saboda haka ashe habaici yana da matuƙar matsayi ko a ce muhimmanci ga al’ummar Hausawa kamar yadda sauran adabin baka suke, wato su waƙa da karin magana da tatsuniya, waɗanda kusan kullum sai an yi amfani da su.
Saboda irin matsayin da habaici yake da shi ga al’ummar Hausawa ya sa ya zama muhimmi a gurinsu ta bangare daban-daban.
Marubuciya:
AZIMA MANSUR AHMAD