HAUSAWA DA SADARWAR INTANET

0 238

SAMUWAR INTANET A NIJERIYA

Samuwar Intanet a Nijeriya idan aka kwatanta da sauran qasashe na duniya, sai a ga cewar tarihin gajere ne. Fasahar intanet ta fara shigo wa Nijeriya ne a shekarar 1990, lokacin da Jamiar Ilorin da ke Jihar Kwara ta samu haduwa da fasahar sadarwar i-mel (e-mail) da taimakon jamiar MC Master da ke qasar Kanada (Canada).

Bayan shekaru uku ne gwamnatin Tarayya ta hada Nijeriya da sauran qasashen duniya da sadarwar i-mel (e-mail) wanda ta Kwalejin fasahar Yaba (Yabatech) da ke Legas ne ake karbar saqonnin i-mel a Nijeriya (www.fasaharintanet.blogspot.com).

Abubakar (2007:23) ya nuna cewar, a fadade dai fasahar intanet ta shigo qasar nan ne kain da nain cikin shekarar 1998 lokacin da hukumar sadarwa ta qasa (NITEL) ta bayar da lasisin kafa mashaqatar tsallake-tsallake (Cyber Café) ga masu shawa, amma ba su fi guda goma ba wadanda suka sami budewa a tsakanin Legas da Abuja. Wannan ce ta sa fasahar intanet ba ta samu kutsa wa qasar Hausa ba, sai wajejen shekara ta 2001, lokacin da ta bulla a Kano.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »