HAUSAWA DA SADARWAR INTANET

0 238

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Abubakar (2007:23) ya nuna cewa, tun wajejen (1995) ne a cikin wani littafi mai suna The Road Ahead wanda shugaban kamfanin Microsoft Bill Gates ya rubuta, ya yi hasashen wannan mataki na dunqulewar duniya ta yadda kowa zai iya sarafa bayanai da ilimin da ya shafi fannonin rayuwa daban-daban cikin sauqi, kuma cikin taqaitaccen lokaci.


Babu shakka, a yanzu duk irin bayani ko ilimin da kake nema, za ka iya samun sa a intanet. Massarafar da ke taimakawa mai bincike wajejen zaqulo bayanai kuwa, ita ce Matambayi Ba Ya Vata (Search Engines). Wannan masarrafa wata Manhaja ce da ke zaqulo nauoin bayanai da ke maqare a intanet ta hanyar shigar da kalma ko kalmomin da suka shafi nauin bayanan da ake so. Sannan a kowace masarrafar akwai hanyoyin neman bayanai iri biyu kamar haka:

  • Hanya ta farko ita ce shigar da kalma ko kalmomi da suka shafi irin bayanin da ake nema kai tsaye zuwa masarrafar zaqulo bayanai, sannan a matsa enter ko go ko kuma search. Daga nan sai amsoshin da suka yi daidai da bayanan da kake nema su bayyana, sai ka zavi daidai da buqatarka.
  • Hanya ta biyu kuma, ita ce inda ake samun kalmomin da suka shafi fannoni daban-daban a jere a jikin allon kwamfuta, sai ka zavi wanda ya dace da buqatarka, misali Education, idan ka matsa, sai ya kai ka inda za ka sami fannonin ilimi daban-daban.

Manya daga cikin Matambayi Ba Ya Vata da ake shiga domin samun bayanai a fannoni daban-daban sun haxa da:

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »