Alhaji Ahmadu Chanchangi, shahararren Dan Kasuwa ne Attajiri kuma mai taimako ga al’umma, an haife shi a shekarar (1934) a garin Taraba, Najeriya. Ya rayu ne a unguwa Tudun Wada, dake cikin birnin Kaduna, inda ya kafa turakun kasuwancin sa.
Marigayin ya mallaki manyan kadarori da suka hada da jiragen sama (Chanchangi Airlines), Ginannun Gidaje, Manya-Manyan Motocin Sufuri, Kasuwanni, da Makarantun neman ilimi.
Duk da wannan tarin dukiyar ta sa, bai sa ya manta da addini ba, ya taka rawar gani sosai wajen gina Al’umma Masallatai, Makarantun Islamiyya, Maqabartu, da Gidajen Marayu, tare da bayar da taimako ga mabukata da gajiyayyu aduk inda suke.
A lokacin jana’izarsa a ranar 17 ga Janairu, 2018, saboda taron jama’a da cunkoso, Mutane shida (6) ne suka zube kasa a suma, wannan wata alama ce dake nuna yadda Jama’a suka ƙaunace shi da girmama aikinsa.
Allah ya jikansa da rahama, ya sanya Aljanna ce makomarsa, shi da dukkan musulmai da suka rigamu baki daya.
Ameen.
