Tarihin Kafuwar Jihar Kano 1967-2020

0 1,763

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Tarihin Kano, gari ne mai daɗaɗɗen tarihi, garin da a wannan shekara (2020) ya kai kimanin shekaru dubu ɗaya da Ashirin da daya (999 zuwa 2020).

Gari ne da ya fara daga sansanin mafarauta a mafi shaharar ruwayoyi, har ya zama katafaren birni sannan ya rikiɗe ya koma masaurauta, sannan ya koma lardi, daga bisani kuma ya zama jaha mafi yawan jama’a a duk faɗin ƙasar Najeriya.

Tarihin Kano

Wannan jaha daga shekarar da aka ƙirƙire ta zuwa yau, ta samu jagorancin gwamnoni har goma sha shida daga shekarar haihuwarta 1967 zuwa 2020.

Akwai gurare masu daɗaɗɗen tarihi a wannan jaha da suka haɗa da duwatsun Dala, Goron Dutse, Magwan, da kuma Dutsen Fanisau.

Sannan kuma akwai muhimman gurare da abubuwan tarihi da suka haɗa da ganuwa da ƙofofin gari, gidajen sarauta, da masallatai waɗanda aka giggina tun zamanin sarakunan baya, marina, majema, da sauransu.

Kasuwanci da sana’a, na zamani da na dauri, kai ka ce ba wani gari in ba Kano ba. Sana’o’in ƙira, farauta, fatauci, wanzanci, ɗinki, jima, rini, da sauransu, duk ana yi a Kano tun daga 999 har zuwa 2016.

Waɗannan sana’o’i su suka haifar da kasuwannin da suka zama manya a Afirka.

Tabbas, ba zai yiwu duniya ta manta da Kasuwar Kurmi ba, haka nan Kasuwar Kantin Kwari, Babbar kasuwar kayan amfanin gona ta Dawanau; ƙwarai, wannan kasuwa ta kere duk sa’o’inta a iya faɗin Afirka.

Akwai wasu kasuwannin kamar irin su Kasuwar Ujile, Kasuwar Mariri, Kasuwar Ƙofar Wambai, Kasuwar Rimi, Kasuwar Sabon Gari, Kasuwar ‘Yan Lemo, Kasuwar ‘Yankaba, da sauransu.

Duk a Kano suke da ma waɗanda ban kawo a wannan rubutun nawa ba.

MANAZARTA:

  • Kano State Ministry of Commerce. (2000). Kano State of Nigeria, Centre of Commerce. An buga a Sagagi Press, Kano.
  • Ɗanyaro M.M. (1997). Kano State 30 Years of Statehood (1967 – 1997).
  • Barau A.S. (2007). The Great Attractions of Kano. Research and Documentation Directorate, Office of the Executive Governor, Government House, Kano.
  • Yakasai T. (2004). Tanko Yakasai, The Story of a Humble Life, An Autobiography, Volume I. Goverment Printers, Kano-Nigeria.

Tarihin Kano

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »