Ayyukan Sana’ar Wanzanci

0 306

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Wanzanci


Gabatarwa
Wanzanci na daga cikin daɗaɗɗun sana’o’in ƙasar Hausa . Sana’a ce da ake yinta ta hanyar amfani da aska da kuma wasu kayan aiki. Sana’ar wanzanci tana da matuƙar tasiri a ƙasar Hausa. Wanzami a zamanin baya matsayinsa iri ɗaya ne da na likita a wannan zamani da muke ciki. Kenan ana iya cewa a da, wanzami shi ke bada maganin cututtuka. Wanzami shi ke yin aski, zane, kaciya, da sauransu.
Baya ga sana’ar aski, wanzami kan gudanar da wasu ayyuka da suka shafi kawar da cututtuka kodai ta hanyar bayar da magani kai tsaye, ko kuma ta hanyar tsaga jikin mutum kamar cire agalawa, ɓalli-ɓalli, ƙaho da sauransu.
Sana’ar wanzanci tana da sarki da ake yiwa laƙabi da Sarkin Aska. A cikin rukunin masu sana’o’in Hausa, babu wanda ya fi wanzami kusa da jama’a.
Aski


Kayan Aiki

 1. Zabira: ita ce jakar wanzamai, a cikinta suke zuba dukkan kayayyakin aikinsu in banda ƙoƙo, da jallon ruwa.
 2. Ƙaho: Ƙaho ne na Saniya ake fiƙe shi a yi masa ƙofa a tsakiya.
  Yadda ake Yiwa Mutum Ƙaho Da farko za a ɗora wannan ƙaho a jikin mutum sai a riƙe shi da hannu, sannan kuma a riƙa zuƙo iska ta wannan ƙofa. Idan wanna ƙaho ya kai matakin da ya kama jikin mutum, to sai a toshe ƙofar da hannu sannan a kawo danƙo a liƙe ƙofar (wannan danƙo kuma daga jikin bishiyar gamji ake samo shi). Can kuma bayan wani ɗan lokaci da ake ganin jinin ya taru a wannan guri da aka kafa wannan ƙaho, sai a cire ƙahon, sannan a ɗauko aska a tsattsaga gurin. Bayan an tsattsaga gurin sai kuma a sake mayar da wannan ƙahon, sannan a sake zuƙo shi, a wannan karon jinin nan da ya taru shi ne zai fara fitowa. Idan ya sake kama jikin mutum to sai a sake barinsa na wani lokaci. Can sai a zo a cire shi a zubar da jinin da ya taru a ciki. Sannan a sake kafa shi a sake zuƙa. Da haka-da haka sai wannan jini ya fice baki ɗaya. Sannan sai kuma a kawo auduga a ɗan gogge jinin da yake jikin mutum. Sai kuma a kawo garin magani a barbaɗa a kan wannan tsaga.
  Amfanin Ƙaho : Ana amfani da shi wajen cire mataccen jini ko ciwon sanyi daga jikin mutum.
 3. Dogari ko Mataki: shi kuma ice ne da ake sassaƙe shi. Ana amfani da shi wajen danne harshe idan za a cire hakin wuya (haƙin wuya wani nama ne da yake tsirowa a jikin ganɗa, sannan kuma yana susar hanƙa. Wannan yakan saka mutum ya ji kamar zai yi amai).
 4. Ƙoshiya: Aska ce mai lanƙwasa wacce ake yiwa ƙota da icce sannan kuma a rufe ƙotar da fata. Da wannan aska ake cire hakin wuya.
 5. ‘Yartsaga: Aska ce ‘yar ƙarama da ake amfani da ita wajen yin tsaga kamar tsagar ƙaho, ɓalli-ɓalli, tsagar fuska, tsaga ƙurji da sauransu.
 6. Aska: Aska wuƙa ce ta wanzamai, da ita ake aski, gyaran fuska, kaciya, da sauran ayyukan wanzamai masu yawa.
  Image
 7. Auduga: Ana kuma kiran auduga da sunan kaɗa a Hausa. Amfanin auduga a wajen wanzamai shi ne share jini. Wato da ita wanzamai ke amfani wajen share jini idan sun yi tsaga.
 8. Mawashi: Kala biyu ne, akwai na dutse, sannan akwai kuma na fata. Shi na dutse irin ƙanan duwatsun nan ne masu kyau da siffa ta musamman ake samu yawanci a cikin kogi ko kuma gidin dutse. Na fatar kuwa fatar tsakiyar gadon bayan akuya ce ake yanke ta a jeme ta ana amfani da ita wajen wasa aska.
  Mawashin Dutse
  Mawashin Fata
 9. Isga: Jelar saniya ce ake yi mata ƙota da icce, sannan kuma dukawa su yi mata rufi da fata.
 10. Sabulun Salo: Ana amfani da shi wajen shasshafawa a suma idan za a yiwa mutum aski ko gyaran fuska. Babban amfaninsa shi ne yakan saka sumar ta yi laushi, sannan kuma zafin askin ya ragu.
 11. Ƙoƙo: A cikinsa ake zuba sabulun salon da kuma ruwa kaɗan a samansa.
 12. Jallo: Buta ce ta duma (ƙwarya), a cikinta wanzamai ke ɗura ruwan aski.
 13. Matsefata: Ana amfani da ita wajen cire sartse.
 14. Ruwa.
  Ayyukan Wanzamai
  Aski
  Tsaga
  Ƙaho
  Kaciya
  Cire Sartse
  Bayar da Magani
  Wasannin Wanzamai
  Wanzamai suna da keɓantattun al’adunsu da suke yi a lokutan
  bukukuwansu , suna kuma da gangarsu ta musamman. Kurya, ita ce gangar wanzamai, bikinsu kuma ana ce da shi Wasan Aska. Idan za a yi wasan aska, akan saka rana da wuri, sai jama’a su tanadi wannan rana domin kallo, su kuma masu gudanar da wannan wasa su yi shiri. Makaɗin gangar wanzamai yakan je filin da za a gudanar da wannan wasa ya fara kiɗa tun da wuri. Idan jama’a suka jiyo sautin wannan ganga, sai su riƙa zuwa gurin sannu a hankali suna taruwa. Bayan jama’a sun taru, su kuma wanzamai sai su zo domin gwada bajimtarsu. Daga cikin abubuwan da suke yi akwai fito da aska ta yi rawa, yin kaciya batare da jini ya zuba ba, yin kaciya daga nesa, da sauransu.

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »