Amfanin Cin Farin Wake Ga Maice Mai Ciki Da Kananan Yara

0 70

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Farin wake yana dauke da wadataccen sinadarin CALCIUM Wanda yake da matukar amfani wajan karawa
Kasusuwa da hakora/haure karfi.

Ana son mace mai ciki ta rika cin farin Wake musamman ma wasu suna sarrafa shi ta hanyoyi da dama kamar : Ayi faten wake, Alala/Alale (Moi-moi), Wake da shinkafa ko a dafa shi haka kawai ba tare da anyi fatenshi ba aci shi shi kadai. Lallaikam duk mai cikin da ta dauki wake a matsayin abincin da take Ci a kusan kullum to za kuga lafiyarta da ta jaririnta sunyi dabam da wacce ba ita ba a lokacin da take da ciki da kuma bayan ta haife cikin.

Bayan cin FARIN WAKE akwai abubuwan da suke ɗauke da sinadarin CALCIUM da Kuma wadanda abubuwa da shawarwarin da ake son mace mai ciki ko mai shayarwa ko kananan yara su rika amfani da su akai akai, su ne kamar haka:

1- Shan Madara ko Nono

2- Arika cin dafaffen Kwai

3-Kubewa ( A rika shan miyar kubewa akai akai danya ko busasshiya).

4- Arika shafawa kananan yara Man zaitun a ƙafafuwan su sbd hakan yana sanya kafarsu tayi kwari sosai har su fara iya yin tafiya da wuri da yardar ALLAH.

5- A rika shafawa jariri Man Tafarnuwa mai kyau a dasashinsa ( saboda rigakafin ciwon fitowar hakori da kuma rage radadin da yara ke ji wajan fitowar haƙoran, kuma zazzabin nan na fitowar hakori da yawan kashi, yaro zai rage yinsu sakamakon amfani da wannan tsarin da yardar Allah.

6- Mai ciki idan ya kai wata 7 tarika dafa : ‘Ya’yan Hulba, da ‘ya’yan Habbatus saudah da Ganyen Na’a Na’a ko ganyen Doddoya tana sha safe da dare har lokacin da za ta haihu, ( Wannan yana matuƙar taimakawa mai ciki sosai kuma yana taimakawa jaririnta ya samu kuzari, kwarin jiki, lafiyar jiki da kuma Basira zaiyi dabam da sauran yaran da ba ayi musu wanna tsarin ba DA YARDAR ALLAH.)

7- Idan mace ta haihu ana so ta rika amfani da abubuwan can da na lissafo a farko, da kuma dafa wadan nan: Kanumfari, Citta da lipton ko dai wani ganyen shayin dabam tana sha safe da rana da dare har tsawon watanni uku. In shaa ALLAHu Yana taimakawa wajan rage mata tumbin da masu jego ke yi, kuma yana kara bude bututun Fallopian tube. Kuma dole sai ta guji shan ruwan sanyi sbd gudun samun matsala a Fallopian tube dinta, domin wasu shan ruwan sanyi yana haddasar musu da Toshewar bututun Fallopian tube kuma su iya samun matsala wajan kara daukar wani cikin bayan sunyi haihuwar fari.

8- Mai jego ana so ta rage cin Abu mai nauyi sbd gudun yin tumbi, ta yawaita shan kayan fruit da ruwan dumi ko kunu
Mai zafi akai akai, sbd suna kona kitsen da mace ke daukowa a yayin dawainiyar juna biyun da sukayi, wanda ke sanya mai jego yin tumbi bayan ta haihu.

Wadan nan kenan., Duk wannan sanadi ne amma Allah na iya yin abinda yaga dama, sbd shi ne Ubangijin kowa da komai.

Allah yasa mudace Kuma yakara mana lafiya mai amfani.

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »