Amfanin Ganyen Dankalin Hausa Ga Lafiyar Jikin Dan Adam

0 766

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Ba iya Dankalin ne ke da amfani ba hatta ganyensa na yana da matukar amfani a jikkunan mu, ga kadan daga cikin amfanin ganyen Dankalin Hausa ga lafiyarmu:

1- Ga masu fama da matsalar gani wadanda ba sa iya gani sosai ko masu fama da ciwon ido ko masu fama da ƙarancin jini to surika amfani da Ganyen Dankalin Hausa,

Yadda za suyi amfani da shi shine kamar haka: A samo wadataccen Ganyen Dankalin Hausa sai a tsaftace shi kuma a mistsike shi a fitar da ruwan, ruwan ne za a rika sha safe da yamma kafin mutum yayi breakfast a gwada haka har tsawon kwanaki 3.

Mai matsalar karancin jini kuma zai sha ruwan ne ko ya hada shi da Madarar gwangwani wanda idan ana neman jini a jikin mutum yan shan wannan hadin nan take kuwa jini zai zo ya malale jikinsa da YARDAR ALLAH.

2- Ga masu fama da Matsalar hawan jini da Diabetics kuwa za su iya amfani da ruwan da aka matse, ko kuma su tafasa ganyen na tsawon mintuna 25 sai a tace a barshi ya huce sai a rika sha akai akai, in sha ALLAH za a samu sauyi sosai.

3- Namijin da yake da matsala a wajan iyalinsa kamar matsalar Infertility , sai ya tafasa ganyen tsawon mintuna 25 sai ya tace shi ya rika sha safe da yamma. In sha ALLAH zai samu lafiya.

4- Ga masu fama da matsalar Diabetics, hawan jini da Cancer kuwa da kuma masu bukatar ƙarin karfin garkuwar jikinsu sai su rika yin miyar ganye da ganyen Dankalin Hausa ( Vegetable soup), wacce za su rika ci akai akai da duk wani abin hadin da suke da bukata, ( Amma kar a bari miyar ta dade a kan wuta har na tsawon lokaci sbd wasu sinadaran da ake bukata za su iya konewa ko ma su bar jikin ganyen.

Wajan mistsikeshi ko tafasa shi ko yin miyar shi, har da icen da Ganyen yake jikinsa ake yin amfani da shi ba zare ganyen za ayi ba abar icen, gaba daya ake amfani da su, sbd shi ma yana da matukar amfani sosai.

Tabbas GANYEN DANKALIN HAUSA yana da matukar fa’ida ga lafiyarmu wannan ma ƙadan kenan daga cikin amfaninsa.

Allah yasa mudace Kuma yakara mana lafiya mai amfani.

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »