Farfadowar Tsumburbura A Kano

0 813



A zamanin sarkin kano Kanajeji, farkon karni na goma sha biyar aka fara yaki da lifidi da kwalkwali saboda barnar da Damagarawa suka yi masa a yakin Bumbutu.

Kanajeji yayi yaki da zazau har yayi sansani a Turunku amma bai samu galaba ba ya dawo kano.sai ya shawarci fadawansa yadda zai samu galaba.



Sarki suri (surin tsumburbura) yace “ Ai sai ka karfafa gunkin nan da kakanka ya lalata “kanajeji yace Yaya zanyi ? Sai sarkin suri ya kawo wani itace ya karya sai ga maciya a ciki aka yanka muciyar akayi takalma da fatar kuma aka rufa dundufa akayi kuntukuru da itacen aka kai can aka jefa cikin Dankwai( wato inda dodon tsumburbura ya kaura lokacin da sarki tsamiya ya rusa dakin sa).



Sarkin suri yayi tsirara ya sanya takalman nan ya kewaya kututururen itacen tsumburbura, yana wakar Barbushe . shi kuwa sarki kanajeji yayi yadda sarkin suri yayi( wa’iyazu Billahi).



Bayan wannan tsafin sai sarkin Kanajeji ya shirya ya koma zazzau , ya nemi sa’a akan su kuma ya samu har saida ya kama sarkin zazzau. Daga nan sai yazo shika ya washe su ya koma gida.


Zamu iya tunawa da sarki kanajeji saboda nasarar da ya samu akan zazzagawa, duk da haka zamufi tunawa da barnar da yayi na komawa da kano kan sha’anin harkar tsafin,masu Bautawa tsumburbura.

Tarihin kano
08027270093

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »