Tarihin San’nar Kira A Kasar Hausa Kashi Na Daya (1)

1 99

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

KIRA:

Sana’ar Ƙira tana daga cikin daɗaɗɗun sana’o’in ƙasar Hausa. Maƙera su ke samar da mafiya yawan kayan aikin da sauran masu sana’o’in Hausa ke amfani da su. Gurin da ake yin wannan sana’a shi ake kira maƙera. Haka nan ma mai yin ƙira akan kira shi da maƙeri (mutum ɗaya kena) ko kuma maƙera (jama’u kenan).

Sana’ar Ƙira sana’a ce da ake sarrafa tama da ƙarafa, zinariya ko azurfa, da sauran dangogin ƙarfe a mayar da su abun amfani wanda ka zama makami ko ma’aikaci (abin yin sana’a).

NAU’IN KIRA KO MAKERA

Makera ko kuma sana’ar Kira din kanta ta kasu kashi biyu. Ma’ana akwai kirar babbaku da ta farfaru.

TA BABBAKU

Babbaku su ne makera na asali da suke sarrafa tama domin samar da karfe ko karafa. Haka kuma su ne Makeran da suke amfani da bakin karfe domin samar da abubuwa daban-daban don tallafa wa rayuwar al’umma ta yau da kullum, musamman Bahaushe. Su ne Makeran da suke samar da abubuwa kamar, lauje da kibiya da matsefata da garma da fatanya da wuka da gatari da takobi da murhu da tebur da kurar guga da kwangiri da dai duk wani abu mai tasarifi da bakn karfe.

TA FARFARU

A daya bangaran kuma, akwai Makeran farfaru, wato makera na farin karfe, wadanda suke amfani da goran-ruwa ko farin karfe domin samar da wasu kananan abubuwa, amma masu muhimmanci ga rayuwar Bahaushe. Ire-iren abubuwan da suke samarwa sun hadar da ludayin sha da ludayin miya da zobba da cokali da sauran kayayyakin karau na adon mata kamar dankunne da awarwaro da kwankwado da sauransu.

Ko ta yaya ma dai, wadannan nau’o’i na Makera sun karbu hannu bibbiyu a cikin al’ummar Hausawa. Haka kuma suna tallafawa rayuwar Hausawa ta yau da kullum, domin samar da abubuwan masarufi da suka danganci ci da sha da sutura da muhalli domin gudanar da sahihiyar rayuwa mai amfani ga daukacin alummar Hausawa.

KAYAYYAKIN AIWATAR DA SANA’AR KIRA

MASKO: Shima karfe ne mai dan tsawo kimanin kamu guda, yana da fadin kai. Zubinsa iri daya ne da masaba amma shi yana da fadin kai, kuma marikinsa a lailaye yake shima ana dukan karfe ne da shi.

HANTSAKI/AWARTAKI: Karfe ne mai kama da almakashi. Wato karfe ne ake gindaya shi da wani karfen, akulle shi a tsakiya, bakinsa yana budewa ya kuma rufe. Da shi ne ake rike karfen da aka dauko daga wuta domin sarrafawa.

KURFI: Karfe ne gajere, kutukurkuri mai fadin kai da fadin baki. Anan amfanin da shi ne domin datse karfe da kuma gutsuttsureshi.

MATSONI: Karfe ne mai dan tsaho da bai fi kamu biyu ba, Yana da tsini daga gindinsa. Haka kuma yana da dan kauri daga kirjinsa zuwa kansa. Da shi ne ake huda karfe.

TURMI: Shima karfene da’irarre mai karfin gaske, yana da yanayi mai zobe. A kansane ake dora karfe domin a huda shi da matsoni.

MADOSHI: Ana amfani da shi ne wajen huda kota kuma iri biyu ne. akwai babba da kuma karami. Karfe ne mulmulalle amma kuma siriri. Yana da kotar itace, kuma da shi ne ake huda kofofi kamar na su fatanya da magirbi, da sauransu.

MAGAGARI: Shi kuma wannan karfe ne mai dan tsaho da fadi. Haka kuma yana da kurzunu – kurzunu a jikinsa. Da shi ne ake wasa ko koda karfen da aka kera ko sarrafa shi. Misali wuka da takobi da lauje da sauransu.

KALAMBA: Karfe ne kantararre da murikai guda biyu, wato dama da hagu yana da kaifin gaske. Da shi ne ake katse karfe idan ya yi tsatsa ko kuma ya yi baki domin a sabunta shi ko kuma

domin ya yi fari ko haske.

GIZAGO: Karfe ne mai karfi da kaifi da ake makala shi a wata kantararriyar kota. Makera na amfani da shi wajen sassake kotoci.

GAWAYI: Konannen itace ne na kirya ko makarho da ake hura wutar kira da shi. Wato yana da kwarin gaske, kuma baya cinyewa da wuri ko konewa.

ZIGAZIGI: Wato wani abu ne na fata kamar jaka. Ana sanya masa wani bututun karfe ne, kuma yana da hannaye ne guda biyu. Da shi ne ake rura wutar yin Kira. Ana hade hannaye ne a bude su domin kwarfar iska, iskar kuma ta rifa fita ta batutun da ke sanye da jikin tubalin bakin wuta, domin rura wutar yin kirar.

TURU NA MAKERA:

 Wannan, ba wani abu bane illa dan wani kwari da ake hura wutar makera a ciki. Wato a nan ne ake zuba gawayi, a kuma zuro tubalin bakin wuta gindin wannan turu na makera domin a rura wutar.

MAKA/MAKATA:

Wani karfe ne baki, mai kwarin gaske wanda yake a da’irance. Ana zura shi ne a makogwaron uwar makera domin ya zamanto tsinin uwar makera bai wuce turu ba. Haka kuma don kada turun ya fashe.

TUBALIN MAKERA /TUBALAN BAKIN WUTA:

Wannan ba wani abu ba ne illa, kasa ce da ake kwaba ta, ta bushe, sannan a yi mata babban baki da kuma kofa a zururu tanan ake sako bakin zigazigin domin hura ko rura wutar makera.

ICCEN BAKIN TUBALI: 

Itace ne na kuka da ake fere shi a kuma daidaita shi domin ya zauna abakin tubalin bakin wuta, ta nan ne iskar zugagigi take biyowa zuwa kwarin makera domin rura wutar yin kirar.

Wadannan abubuwa da aka zayyana a baya, su ne kayayyakin da ake amfani da su domin gudanar da sana’ar kira. Ita dai wannan sana’a ta kira sana’ace ta maza, akasari kuma sun gada ne daga kaka da kakanni, haka kuma mata na yin ta amma ba su yi wata shahara a kanta ba, domin a kasar hausa daga mace ta kai wani munzali na shekaru, takan zauna ne a gida har lokacin gabatar da ita ya yi, sannan akai ta gidan mijinta.

DAGA:

Tsangayar Daukaka Harshen Hausa Da Al’adu Da Kuma Adabi, da kuma

RubunIlimi.

MANAZARTA

Musa H. Modibbo, (1979): “Ciniki da Sana’o’I a Kasar Hausa”. General Editor; Ibrahim Yaro Yahya. Thomas Nelson Publishers.

Muhammad Abdu Durumin-iya (2006) “Tasirin Kimiyya da Kare- karen Zamani A kan Sana’o’in Hausawa na Gargajiya”. Kabs Print Service (NIG).

Aminu M.S (1993) “Faduwar Sana’o’in Gargajiya a Zamanance”, Kundin Binciken na neman Digiri na farko.

Tattaunawa da Mallam Umaru Makeri da ke unguwar Yamadawa, ranar Talata 16th-09-2014, da misalign karfe 5:30

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

  1. […] da sana’a, na zamani da na dauri, kai ka ce ba wani gari in ba Kano ba. Sana’o’in ƙira, farauta, fatauci, wanzanci, ɗinki, jima, rini, da sauransu, duk ana yi a Kano tun daga 999 har […]

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »