MAZAUNA KANO NA FARKO
Mazauna Kano Na Farko A karshen karni na Tara 9th century na masihiyya wadan su, wadanda babu hakikar daga ina suka fito sosai, amma dai wajen Arewa suke ,suka zo suka zauna akan duwatsun dake kewaye da sararin da yanzu ake Kira kano.irin duwatsun nan sune irin su Dala Gwarran dutse,duten magwan da na fanisau.
Wadannan mutanen an hakikacen cewa maharba ne, suna farauta a wani kurmi Wanda yake shine tushen Rafin jakara ,inda Kasuwar kurmi take a yanzu.kano ta samu sunan ta daga wadanan maharban suka jarraba Dan noma suka ga wurin yana albarka ,sai suka cigaba da zama, suka ringa yake daji suna gonaki.albarkar wajen mai ban mamaki sai ta jawo wadan su mutanen daga wadan su guraren suna zama.
Da taron mutane suka fara yawa sai suka yi shugaba, Wanda a bisa al’ada mutanen wannan lokacin mutum yana zama mai fifiko ne bisa idan yana da karfin zafi.
Babu hakikanin akan irin tsarin mulkin da wadannan al’ummar suka Gina shhgabancin su. Amma duk da haka za’a iya cewa aikin shugaba a wannan lokacin bai wuce tsara dokokin farauta ba da kusaci da tsafi da mutane ke bautawa ba.
Tarihin kano
08027270083