Zazzabin maleriya cuta ce wacce mafi akasari tafi addabar ƴan Afrika, kasancewar rashin gyara magudan ruwa, mahalli da kuma barin ƙazanta ko Datti a ko ina, wanda hakan yake bawa sauro damar zama a waɗannan wurare yayi ta zuba ƴaƴa wanda da zarar dare yayi sukuma su addabe mu ta ko ina.
A yau ma kamar kullum bayani ne game da maganin zazzabin cizon sauro,wanda a wannan lokaci yake addabar jama’a, insha Allahu wanda hanya tana magance wannan ciwon cikin kankanin lokaci da yardar Allah,kuma a samu sauki.
Akwai alamomi da mutum zai gane ya kamu da Zazzaɓin cizon sauro sune kamar haka.
Zafin jiki,
Ciwon kai,
Rashin jin da]in cin abinci,
Kasala,
Amai,
Gudawa,
Tafiyar ruwa (Convulsion),
Alamun rashin isasshen jini,
Kakkarwa,
Ramewa,
Suma.
Hanyar da za’a magance wannan cuta shine. A samu.
- Bawon Abarba,
- Lemon tsami,
- ruwa.
Lemon Tsami
Bawon Abarbar Ake Buƙata
Yadda Za’a Haɗa
Za’a samu bawon Abarba daidai misali lemon tsami rabi idan yana da girma idan kuma bashi dashi sai a saka guda daya, da ruwa kofi 4.
Da farko za’a wanke bawon sannan a zuba a tukunya a yayyanka lemon tsamin a zuba harda bawon a ciki, sannan a dafa na minti 30.
Bayan an sauke sai a zuba a filas,a rika shan kofi ɗai ɗai har sau 4 a rana ga babbam mutum.
Yaro daga shekara 7 zuwa 12 zai sha rabin kofi sau 2 a rana.
Tsawon kwana 3 insha Allahu zaa samu sauki.
Daga: (DR) maijalalaini.