An haifi Rahama ranar 17 ga watan Disamba alib 1993 a garin Kaduna tare da mahaifinta Alh. Ibrahim Sadau, Rahama tauraruwa ce a film din hausa da turanci kuma yar rawa, Rahama tayi gasar rawa iri daban-daban tun tana karamar yarinya lokacin tana makaranta.
Haka zalika tauraruwa Rahama Sadau tayi karata Business Administration a kaduna Polytechnic, sanan kuma tana jin yaren Indiyanci sosai da sosai.
Rahama Sadau, sunanata ya daukaka ne a karshen shekara ta 2013, watanni kadan bayan shigarta masana’antar shirya fina-finan Hausa wato kannywood yayin da aka hausaka ta a wani fim mai suna Gani ga Wane, fim dayake na daya a cikin fitatun fina finai, kuma wannan fim shine farkon fim dinta data fara yi.
LAMBAR YABON DATA SAMU:
- Rahama Sadau tasamu nasarar cin Tauraruwa ta farko a City People Aword a 2014.
- Haka zalika Rahama Sadau tasamu nasarar cin tauraaruwar Afrika wato the 9th african Film Aword By African Voice.
DAKATARWAR DA AKAIWA TAURARUWAR A HAUSA FIM.
Rahama Sadau andakatar da ita a hausa fim daga kungiyar tace fina-finan Hausa wato MOPPAN a ranar Lahadi 2 ga watan oktoba sakamakon wata runguma da akayimata a wata bidiyon wakar Hausa, wanda wani mawakinHausa dan Jos mai sun Classiq yay mata.
Sainsa ta faru a kungiyar ta MOPPAN kasancewar rungumar da jarumar tayiwa mawakin Classiq a wakar tasu wanda hakan suka ce haramun ne a dokokin kungiyar tasu, Hakan kuma yajawo kace nace ga musulman kasar baki daya.
GA WASU DAGA CIKIN TAMBAYOYIN DA JARUMAR TA AMSA.
Rahama Sadau na daya daga cikin ’yan fim din Hausa da ke tashe. Haifaffiyar Jihar Kaduna ce ita. Baya ga kwarewarta wajen wasa kuma ta kasance gwana wajen iya magana da harshen Indiyanci, kamar kuma yadda ta kasance gwana wajen iya taka rawa. A kwanakin baya ne kafar watsa labarai ta intanet, Premium Times ta gana da ita, inda ta bayyana abubuwa da dama da suka shafi rayuwarta da kuma sana’arta. Ga yadda ganawar ta kasance, a sha karatu lafiya:
- Menene abin da ya ja hankalin ki shiga harkar fim?
RAHAMA- Tun ina karamar yarinya nake sha’awar fim kuma nake sha’awar in zama ’yar fim. A lokacin da na girma kuma damar shiga fim ta zo mini, ban yi wata-wata ba, kawai sai na rungume ta. Na fara sana’ar fim.
- Wadanne irin kalubale kika fuskanta a lokacin da kike son shiga harkar fim?
RAHAMA- A lokacin da na shaida wa mahaifiyata kudurina na son shiga harkar fim, ba ta so ba, domin kuwa hankalinta bai natsu da harkar ba. Haka kuma, ba ta son in yi nisa daga kusa da ita, kasancewar ta san ’yan wasan fim kan yi tafiye-tafiye zuwa garuruwa daban-daban, har ma da wajen jihohinsu na ainahi, domin daukar shirin fim. Duk da haka, bayan wani lokaci ina ta tuntubawa, sai ta amince mini da in shiga.
- Wane fim ne na farko a cikin fina-finan da kika fito a cikinsu?
RAHAMA- Fim din ‘Gani Ga Wane’ shi ne na farko da na fara fitowa a cikinsa. Ina kaunarsa sosai saboda na fito cikinsa tare da Ali Nuhu, kuma ba sai na fadada maka bayani ba, ka san abin da nake nufi; a ce mutum ya fito fim tare da Ali Nuhu, a duniyar fina-finan Hausa.
- Wane dalili ya sa Ali Nuhu yake burge ki?
RAHAMA- A gare ni, Ali nuhu shi ya fi kowane dan wasa burgewa da kwarewa kuma shi ne ubangidana a harkar fim. Shi ya koya mini harkar fim ko kuma ma yake kan koya mini. Na dade ina da burin in ga cewa na fito fim tare da shi kuma sai gashi burina ya cika, fim dina na farko, sai gashi na fito tare dashi.
- Kin kasance ’yar rawa, ko har yanzu tana taka rawa?
RAHAMA- A’a. a yanzu na daina yin rawa. Na dauki lokaci mai tsawo da daina rawa.
- Ko za ki dawo ki ci gaba da taka rawar Indiyawa?
RAHAMA- A’a, ba zan ci gaba ba, sai dai kuma a cikin fim. Duk aikin fim din da aka ba ni, idan dai har an bukaci in yi rawa a wata fitowa, zan taka ta sosai, daidai iyawa ta.
- Wane fim ne ya fi ba ki wahala cikin fina-finan ki?
RAHAMA- Fim din da ya fi ba ni wahala, kuma na fuskanci babban kalubale a kansa, shi ne ‘Dogon Zamani.’ Fim din yana cike da kalubale, domin kuwa furodusansa yana son ganin komai ya zama ingantacce a cikinsa. Dalilin haka ya sanya muka wahala kwarai wajen shirya shi.
- Wane shirin fim kika fi sha’awar fitowa?
RAHAMA- Ni na fi son in fito a cikin fina-finai masu ilimantarwa da nishadantarwa. Haka kuma ina son fim mai dauke da rawa da waka.
- Wane dan wasan waje kike son yin fim da shi, idan kin samu dama?
RAHAMA- A rayuwata, ina son haduwa da ’yar fim din Indiya, Priyanka Chopra. Don haka idan na samu dama, ina son in yi fim tare da ita. Idan na samu wannan dama, lallai burina ya cika.
- Wane dan fim ya fi burge ki cikin ‘’yan fim din Kudancin Najeriya?
RAHAMA- ‘’Yar wasar da ke matukar burge ni a Kudancin Najeriya, it ace Tonto Dikeh.
- Wane fim ne ya fi burge ki?
RAHAMA- Fim din ‘Sabuwar Sangaya’ shi ya fi burge ni. Ina matukar sha’awar fim din.
- Cikin mawakan fina-fina Hausa, wane ne ya fi burge ki kuma kika fi so?
RAHAMA- Nazifi Asnanic, Umar M. Shareef da Nura M. Inuwa
- Ko wadanne bangarori kike son ki ga an bunkasa a fina-finan Hausa?
RAHAMA- Duk wani al’amari na rayuwa yana son a bunkasa shi kuma a inganta shi. Saboda haka, ina ganin akwai bukatar tallafi daga gwamnati. Idan aka samu wannan tallafi, za a samu bunkasa shi.