YADDA ZAKI SHIRYA FINKASO

0 834

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Finkaso wani nau’I ne na abinci da hausawa da kuma wasu nau’Ikan yare ke ci, wasu kanci a matsayin abinci wasu kuma kanyi amfani dashi wajen biki ko suna kodai wata muhimmiyar walima data taso.

KAYAN HADI

  • Alkama (kamar gwangwani hudu)
  • Filawarki (gwangwani daya ko biyu)
  • Ruwan tsamiya (kamar Rabin gwangwani)
  • Yeast (cokalin shayi)
  • Sikari (cokali daya) idan ana buQata
  • Ruwan kanwa (cokali daya)
  • Mansuya (kwalba daya ko fiye da haka)

YADDA ZAKI HADA

Kisami robarki mai murfi ki zuba sikariki da da yeast da ruwan tsamiya da kanwa kamar yadda na auna miki filawarki ki hadata da garin alkamarki idan yeast ya narke kijuye filawarki ki kwaba sosai ki tabbatar ba gudaji kuma kar kwabin yayi ruwa karkuma yayi tauri tikiki saiki rufe ya samu kamar awa daya zakiga ya tashi ki dora manki yayi zafi sosai ki sami kwabin ki kara juyashi sosai zakiga ya koma ya kwanta kuma zakiga ayayin da kika dada juyashi kwabin ya dada sakin jikinsa saiki sani dan farantinki ki shafe da ruwa kirika gutsurar kullin kina sawa akan dan farantin ki huda tsakiya saiki saka acikin mai zakiga yana dagowa yana fadawa cikin mai a hankali da kulawa abin

Lura shine funkaso bayason yawan juyawa idan kinga kasan ya soyu saiki juya saman shima ya soyu kuma funkaso bayason mai kadan wajan suya yafison mai wada tacce ya sakata ya wala amfanin tsamiya a funkaso shine bazai taba sha miki maiba kuma zai miki suya tai ja tayi kyau wannan shine iya awon danayi idan da yawa zakiyishi to haka zakirika aunawa kina kara yawan abinda na lissafo miki uwargida ko amarya dafatan zaki nutsu wajan gwaji.

Aci dadi lafiya ina fata zaki turashi zuwa wasu shafikan don yan uwanki su amfana.

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »