Takaitaccen Tarihin Dakta Mariya Mahmoud Bunkure.

0 408

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Dakta Mariya Mahmoud Bunkure likita ce kuma tsohuwar kwamishiniyar ilimi mai zurfi a jihar Kano a Najeriya.

 An haifi dakta Mariya Mahmoud a karamar hukumar Bunkure a jihar Kano a shekarar alif 1976. Ta yi makarantar firamare ta Bunkure Gari, sannan ta wuce GGASS T/ Wadan Dankadai domin yin junior sakandare, sannan ta yi makarantar kimiyyar mata ta Garko. Ta kamala a shekarar alif 1995. Daga nan ta tafi Kwalejin Nazarin Gyaran karatu inda ta rubuta jarabawar  IJMB a shekarar alif 1996.

A shekarar alif 1997 ta samu admission zuwa karatun likitanci a Jami’ar Bayero Kano. Daga nan kuma ta ci gaba da karatun ta har ta zama mai ba da shawara a fannin likitancin iyali a asibitin koyarwa na Aminu Kano.

Dokta Mariya kwararren likita ce ita kuma mai ba da shawara ce a fannin likitancin iyali kuma tana da gogewa sama da shekaru 20 a fagen. Ita memba ce ta National Postgraduate Medical College da kuma Kwalejin Likitoci ta Yammacin Afirka. Baya ga aikin likitancinta, Dokta Mariya ma’aikaciyar gwamnati ce.

 An nada ta a matsayin kwamishiniyar ilimi mai zurfi a jihar Kano a shekarar 2020 zamanin tsohon Gwamnan Jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje. A wannan aiki, ita ce ke da alhakin kula da harkokin Ilimin manyan Makarantu na Jihar Kano.

Dokta Mariya na ɗaya daga cikin Mamba a kungiyoyin mata da dama, kuma ta kanyi magana kan mahimmancin ilimi ga ya’ya mata. Haka kuma ta kasance abin koyi ga mata matasa a jihar Kano.

mariya mahmoud bunkure

Dakta Mariya mace ce mai kwazo da kishin al’umma. Ta himmatu wajen inganta harkar ilimi a jihar Kano da samar da damammaki ga matasa domin samun nasara. Tauraruwa ce da ke tasowa a siyasar Najeriya kuma ta tabbata za ta yi tasiri sosai ga makomar Jihar Kano.

Dakta Mariya tana da aure da kuma  ‘ya’ya hudu. Kuma Mijinta dan kasuwa ne.

A rana 3 ga watan Agusta na shekarar 2023 ne Shugaban kasar Najeriya Bola Tinubu ya sanya Dakta Mariya Mahmoud Bunkure a cikin ministocin da za’a tantance, daidai lokacin da aka cire sunan Dakta Maryam Shatty daga jerin ministocin.

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »