Ado Isah Wanda akafi sani da Ado Gwanja, An haifeshi a ranar 22 ga watan Janairu shekarar alif 1990 a Unguwar Birged da ke birnin Kano, yana ɗaya daga cikin mawakan Arewa dake Najeriya, kuma babban jarumi a masana’antar fina-finan Arewacin Najeriya da aka fi sani da Kannywood.
Yayi karatun Firamare a Makarantar Babbangiji da ke Kar-kasara. Sannan ya yi Sakandare a Ƙofar Nasarawa. Gwanja bai ci gaba da karatu ba, amma yakan je kasuwa wurin mahaifisa kafin ya rasu.
Asalin mahaifin sa dan garin Warawa ne dake wajen Kano, mahaifiyar sa kuwa Shuwa Arab ce daga garin Maiduguri a Jihar Borno dake Najeriya.
Gwanja sau da yawa an fi saninsa a waka fiye da harkar fim, Gwanja ya kware a wakokinsa na mata, ana gayyatarsa zuwa bukukuwa inda yake rera wakokinsa mata na rawa. Tsohon mawakin Hausa Aminu Mai Dawayya na ɗaya daga cikin iyayen gidan Gwanja
Gwanja dai ya fara fitowa a fina-finan Hausa a shekarar 2017, amma ya dauki tsawon lokaci a harkar waka kafin ya fara wasan kwaikwayo.
Wasu daga cikin fitattun wakokin Ado Gwanja sun haɗa da Kujerar Tsakar Gida, Mamar-Mamar, Ɗakin Ba daƙuwa, Asha Rawa-rawa, Kilu ta Ja Bau, Kidan Mata, Warr, Chass, Luwai, da dai sauransu.
Ado Gwanja ya samu lambobin girmamawa da dama a harkar waƙa da fim.
Gwanja yayi aure a shekarar 2018 kuma yana da ƴa guda ɗaya, sai dai kash sun rabu da matar tasa ta farko. A ranar 21 ga watan July shekarar 2023 ne Gwanja yayi sabuwar Amarya.