Takaitaccen Tarihin Adam Abdullahi Adam (Abale)

0 1,054

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Adam Abdullahi Adam wanda akafi sani da Dady “Hikima /Abale /Sand, an haifeshi ne a garin kano kuma yayi karatunsa na Addini da boko duk a cikin garin kano.

YADD YA TSINCI KANSA A HARKAR FILM
Shigarsa harkan film ya shiga ne da wasu sab gogi ba wai yin acting ba abubuwan da yakeyi kuwa shine;

  1. Crew.
  2. Continuity (Cigaban Shiri).
  3. Set Designer ( Mai Tsara wuri ).

Hasalima shi a burinsa da harkan film shine ya zamo Director sakamakon yana harkan kuma yana karatu Abin ya zaman masa biyu, amma a hakan ya kokarta yana taba kowanne yana karatunsa kuma yana harkan film.

ABINDA YA KARANTA A FANNIN ILIMIN SA NA BOKO

Dady hikima wanda akafi sani da Abale ya bayyana Abinda ya karanta a tattaunawan sa da manema labarai inda yace yayi karatu a fannin lafiya inda yace a yanzu shi Nurse ne, sannan ya bayyana yana aiki a asibiti amma saboda harkan film da yake kuma ba’a hadiye taura biyu a baki daya idan ya sami lokaci yana zuwa yayi aiki kyauta sadaka bawai a matsayin ma’ai kacin da ake biyansa albashi ba, kuma saboda skills nashi kada ya manta wasu domin indai ka’iya abu kuma baka dan jarraba yinsa lokaci bayan lokaci wani abin zai iya fita kanka.

SHIN YANA DA AURE.

A tattaunawan da aka yi dashi ya bayyana cewa bashi da Aure Amma idan Allah ya kawo lokaci zaiyi domin komai da lokacinsa.

BABBAN BURINSA.
Ya bayyana cewa tabbas ko wanne dan Adam akwai burinsa a rayuwa, domin ko babban dalilin da yasa ya zabi zama Nurse shine yanason wata rana ace yazama military Nurse (Ma’aikacin Aikin Jinya na sojoji) Don a yanzu inda ya kammala rayuwarsa na harkan film da zaran ya kammala hada digiri (Degree) dinsa Gidan soja zai kada.

ABINCIN DA YAFI SO
Ya bayyana cewa a duniyar abinci yafison nama kayan ciki, da ganda domin indai ganda taji romo ae shikam anyi mai komai

JARUMAR DA TAFI BURGESHI A KANNYWOOD
Abale ya bayyana Aisha Aliyu Tsamiya a matsayin kwanarsa a kannywood domin kuwa ta bashi support sossai a harkan sa na film, shida ita one love ne kawai,

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »