Bani Da Lafiya Kashi Na Tamanin (80)

0 341

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Malamar na gama lissafo abubuwan nan sai kowa a wurin yayi kabbara tare da Addu’ar Allah yasaka da alkhairi.

Ummu Labeeba ta waigo wajan da su Labeeba ke zaune tana cewa Labeeba: Ince dai kuna rubuta abubuwan nan da malama ke magana akai Ko?

Labeeba: Kwarai kuwa Umma ai musamman ma da akazo kan gabar nan, sai na ware shafuka na musamman domin na san akwai abubuwan da za mu karu a ciki sosai.

Itama Ummu Bareerah tace: To ke Bareerah ya banga ke kina dauka ba?

Bareerah: A’a Umma ina dauka mana ga littafin da nake rubuta bayanan nan a gefe na.

Mai gabatarwa yace: To malama munji kin lissafo abubuwan nan masu matukar amfani sosai, amma kuma ya yakamata ayi amfani da su kuma ta hanyar da ta dace da shari’ar Allah ba tare da anyi tsallan badake ba?

Malama: Insha ALLAH kuwa abinda nima nake ta so na fahimtar da al’umma kenan domin akwai wasu masu cakuda kyawawan abubuwa ta gurbatacciyar hanya. misali:

Ka ga dai wadan nan Alqur’ani ne da sauran maya-mayen nan da na lissafo duk abubuwa ne wadanda amfani da su ya halasta, amma sai kaga suna amfani da su ta haramtacciyar hanya tayadda za su rika sako shirke-shirke iri-iri da Tsubbace-tsubbace kala-kala da sauransu, sai su yaudari mutane da cewa: Ai Alqur’ani ne , ai Man Zaitun ne, ai kaza kaza kaza ne, nan kuwa sun cakuda gaskiya da karya…

Amma kaitsaye dai yadda ake amfani da abubuwan nan ga mace mai ciki shi ne:

Za a samu Man zaitun ne da na Habbatus saudah sai a karanta Alqur’ani a ciki musamman Suratul Fatiha, Ayatul Kursiyyu, Suratul Kafirun, Ikhlas, Falaqi da kuma Nasi iya adadin da mutum zai iya a cikin maya-mayan.

Sai a samo Jan Misk ko Bakin Misk ko Miskil Ka’aba , amma Miskil Ka’aba zai fi su tasiri insha ALLAH, sai a karanta wadannan Ayoyin da Surorin a cikinsu ko

“Ammafa mu sani cewa shi Alqur’ani gaba dayansa ya tattaro dukkanin waraka da rahama amma ga wanda yayi imani da shi kadai, kuma babu abinda zai karawa wanda baiyi imani da shi ba sai dai harasa. Ba wai sharadi ne sai iya ayoyin nan da na lissafo ne ake iya karantawa ba a’a, za ka iya karanta wasu Ayoyin da Surorin ma bayan wannan wadanda na lissafo, bukata dai kayi karatun da Khushu’i da tadabburin ma’anoninSA. Allahu A’alam.”

(Insha ALLAH a rubutu nagaba za muji yadda ake amfani da su.)

Allah yasa mudace Kuma yakara mana lafiya mai amfani.

Har kullum mu rika tabbatarwa da zuciyar mu cewar: Magani sila ne na waraka amma ba shi da ikon warkarwa, Allah ne kadai mai iya warkar da wanda yaga dama a duk lokacin da yaga dama, shi kadai ne abin dogara ba maganin ba.

(Ayi mana Addu’ar ALLAH ya yarda da mu da ayyukanmu kuma ya lullube mu da RahamarSA.🤲🏻)

Domin karin bayani:
👇👇👇

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »