Bani Da Lafiya Kashi Na Sabain Da Tara (79)

0 525

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

“Duk da cewar yin maganin ya halasta a shari’ar Muslunci, amma kuma Haramun ne mutum yabi haramtacciyar hanya domin yayi magani ko yayi maganin da duk abinda yake hramun ne ko najasa ne.”

Malamar tace: Ai abin nan a fili yake domin Annabi Sallallahu alaihi Wasallama ya bayar da umarnin ayi magani amma ya ce : Kar ayi magani da ( abinda yake) haramun. Kamar yadda yazo a hadisin Aby Huraira ( Allah yakara masa yarda) wanda Imam Ahmad da sauran As’habul Sunan suka rawaito shi .

Malamar taci gaba da cewa: Wannan haramcin yana kara tabbatar mana cewa : Duk wani maganin da za muyi to mubi hanyar halal ba ta haram ba kuma kar mu kuskura muyi amfani da abinda yake haramun ne wajan yin maganin cututtukan mu, musamman ma wurin neman kariya daga abinda muke kuwa tsoro.

Duk wani magani ya halasta kayi amfani da shi matukar ba haramun bane shi ko hanyar da aka samo shi ko hanyar aikata shi haramun ce kamar : Maqala wani abu ko rataya shi kuma a dogara da shi har a rika mantawa da Allah ne zai iya karewa ba wannan abin ba. Da sauran abubuwan da wasu masu magani ke cewa:

 • Ai idan har mace ta daura wannan abin a qugunta to ba abinda zai cutar da cikinta, ( Kuma wannan abin babu komai a cikinsa sai rubutun sunayen aljanu ko wasu surkulle).
 • Idan mace tana yin tsarki da kaza da kaza ( a fadi wani haramtaccen abu ) ace yana bayar da kariya.
 • Ko su baiwa mace wani surutai da sunan ai addu’a ce , wanda ko su kansu basu san ma’anar abin ba balle ke wacce za ki karanta, kawai sunayen wasu aljanu ne suke rubutawa da Ajami don a rikitar da jahilai ko wadanda Shedan ya batar da su. Da sauransu….

Duk wadannan HARAMUN ne mutum yayi anfani da su da sunan magani domin bata ne kuma hakan ka iya sanya mutum ya hadu da fushin Allah tun anan duniya kuma Allah ya jefa mutum cikin jahannama matukar bai tuba ba har ya mutu. Allah ya kyauta.

Malamar taci gaba da cewa: Amma akwai wasu abubuwan da bincike ya nuna cewa Shedanun Aljanu ba sa son su musamman ma wadanda suke zaune a mahaifar mutane, abubuwan nan su ne kamar haka ga wasu daga cikinsu:

 • Alqur’ani
 • Man Zaitun
 • Man Habbatus saudah.
 • Citta
 • Jan Misk
 • Bakin Misk
 • Qustul hindi ko Qustul Bahary.
 • Miskil Ka’aba

( Insha ALLAH a rubutu nagaba za muji yadda yakamata ayi da su.)

Allah yasa mudace Kuma yakara mana lafiya mai amfani.

Har kullum mu rika tabbatarwa da zuciyar mu cewar: Magani sila ne na waraka amma ba shi da ikon warkarwa, Allah ne kadai mai iya warkar da wanda yaga dama a duk lokacin da yaga dama, shi kadai ne abin dogara ba maganin ba.

(Ayi mana Addu’ar ALLAH ya yarda da mu da ayyukanmu kuma ya lullube mu da RahamarSA.🤲🏻)

Domin karin bayani:
👇👇👇

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »