Takaitaccen Tarihin Sheikh Adam Albanin Gombe

0 434

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Sheikh Adam Muhammad Albanin Gombe an haife shi a shekarar alib 1978 a karamar hukumar Ajingi dake Jihar Kano, sunan mahifin sa Mal. Muhammad Murtala babban Malami ne mai koyar da alkura’ani mai girma.

Ya zauna a Bacirawa dake cikin birnin Kano, yayi karatu a wurin Mal. Garba wanda baida yatsu. Daga nan ya wuce garin Gombe, bisa wasiyar mahaifin sa da yay masa akan cewa idan ya rasu ya tafi wurin kakansa na wajen uwa mai suna Mal. Abdulhamid wanda ake masa lakabi da mal. Karami dake garin Gombe , wanda a wurinsa albanin Gombe yaci gaba da karatun Addini.

Yayi karatunsa a Government Arabic College dake garin gombe, ya kamala a shekarar 2007. Yayi karatunsa na Diploma akan Arabic Education.

Yadda Yasamu Lakabin Albanin Gombe.

Ya samu Albanin Gombe ne kansancewar jin Karatuttukan Marigayi Sheikh Auwal Albani Zaria da kuma haddar su da kuma yin bayanin su ga dalibansa kamar yadda Sheikh Albani Zaria ya keyi da kuma sanya madogarar Karatun/Bayanin nasa ga Sheikh Albani Zaria.

Ta haka ne Daliban sa da kuma Abokan sa suke kiransa da Albani, A lokacin da yasamu damar ziyartar Sheikh Albani Zaria a gidan sa shi da abokan sa dake Zaria bayan gama tattaunawar su shi da sheikh Albani Zaria sai sheikh din ya tabbatar masa da cewa shi Sheikh Adam Muhd Shine Albanin Gombe Shi kuma sheikh Auwal Albani yace shine Albanin Zaria.

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »