Rayuwar Fateema (kashi na daya 1 Hausa Novel)

0 315

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

20221111_190419.jpg

RAYUWAR FATEEMA part 1 (True Life Story)

Rayuwar fateema

Part 1 (Babi Na Daya)

ZARIA yau asabar gobe daurin auren Abbanmu umma tace Abdulrazaq? Nace Na’am Umma, Sai ta kira Sunan Kanwata Phateema, Sai ta amsa, Sai umma tace” saboda haka banaso kuyi wani abu da zaisa wani ko wata yace baku da tarbiyya inaso ku kasance masu nuna farin cikinku akan wannan al’amari, gaba daya muka amsa da cewa to umma “Tace allah yayi muku albarka, mukace amin, abbane ya shigo megadi na binsa da akwatuna, megadi ya aje ya fita, abba yace sannunku da zaman gida, Muka amsa gaba daya yauwa abba, yasa hannu yajanyo akwatunan nan ya bude, kayane niki niki aciki yace hajiya wannan nakine,


Umma ta nuna farin cikinta sosai nida Kanwata aka bamu namu kayan amma fa mu bamu nuna farin ciki ba, Yau litinin kwanan amarya daya a gidan abba, umma ta tura Ni da Phateema Muje mu gaida amarya, Phateema ce tafara shigewa gaba muka shiga bangaren amarya muka tarar abba yana dakin Phateema tace aunty good morning, amarya tajuyo ta kalli Phateema a wulakance tace ke dama a tsaye kuke gaida uwarku? Ni ne nace daga gaisuwa saiki zagi ummarmu to wallahi badai uwarta ba, amarya tace kai dan uwarka ba’a koya maka arbiyya ba? Nace badai uwata ba, amarya ta juya wajen abba alhaji yanxu kanaji yaron nan yana zagina?

Abba baiyi wata-wata ba ya daga hannu ya zabga man mari, Muka juyo a gigice domin abin ya matukar bamu mamaki kasancewar abba ko tsawa bayaso ayi muna amma da mamaki gashi yau shine ya daga
hannunsa ya mare Ni, nan take ta fashe da kuka domin abin ya tsoratata, mukayo waje Phateema tana kuka, umma ta taho da sauri tatare mu tana tambayarmu lafiya?


Phateema ce tayi mata bayanin abinda ya faru’ abba ya fito a fusace yana ta kwala wa umma kira’ umma ta amsa’ abba yafara magana cikin fada, ke tsabar rashin mutunci shine zaki turo wadannan yaran naki suzo suyiwa amaryata rashin mutunci? Umma tace alhaji anya kuwa acikin hayyacin ka kake?

Ke ni kikeyiwa wannan tambayar to wallahi sai nayi maganinku duk wanda yace zai tabamin
amaryata bazamu zauna lafiya dashiba agidannan, abba ya fice a fusace, duk abinda yake faruwa amarya tana tsaye tana yiwa umma dariya’ Nine na xabura da niyar dukan amarya amma umma tai caraf ta rike hannuna tajamu mukayi daki muka bar amarya atsaye tana yimana dariyar mugunta amarya tace kadan kuka gani indai nice sai kunbar gidannan,

KADUNA N.D.A
yaya Mujaheed shiga damuwa matuka kasancewar rashin ziyarar da su abba basu kawo masaba kullum sukai waya da umma sai tace masa suna nan zuwa har ya gaji, dama ba’a maganar abba wanda idan ya kirasa baya daga wayarsa hakan yasa ya tambayi umma lafiya abba baya daga waya ta? Amma sai umma tace masa lafiya aikine yake hanashi kula da kiran da ake masa, duk da haka Yaya Mujaheed yana xargin akwai abinda yake faruwa agidanmu dan haka yake ta fatan karasa shekara dayan data rage masa. a N.D.A domin yaxo gida yaga abinda yake wakana agidanmu……


MUHADU A PART 2

Sarki Ne 👑

Ab Kudancy

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »