Takaitaccen Tarihin Mal. Aminu Ibrahim Daurawa

0 1,226

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

An haifi Mal. Aminu Ibrahim Daurawa a ranar 1 ga watan Janairun, shekarar alif 1969 a cikin iyalan Sheikh Ibrahim Muhammad Bilal wanda aka fi sani da Mai Tafsiri da mahaifiyarsa Hajiya Sa’adatu Mustapha a Gidan Zakara-Mai-Neman-Suna Unguwar Fagge. Jihar Kano.

Mahaifinsa malamin addinin Islama ne kuma tela, yana koyarwa da yamma bayan ya dawo daga wurin aikin sa, mahaifiyarsa kuma ‘yar Bachirawa ce a karamar hukumar Ungogo a jihar Kano.

Aminu Daurawa yayi makarantar kur’ani ta islam tun yana karami wanda hakan ya ba shi damar haddace kur’ani baki daya yana dan shekara 14. Daurawa ya kuma halarci makarantunsa na firamare da sakandare a Kano.

Aminu Ibrahim daurawa
Daurawa 2022

Aminu Daurawa babban malamin addinin Islama ne a Najeriya a cikin kungiyar Izala, ya kafa kungiyar Hisbah a Kano kuma ya zama shugabanta na farko.

Babban burin kungiyar ta Hisbah shi ne kawar da fasikanci a tsakanin al’umma musamman a tsakanin musulmi. (Masu bin addinin Musulunci) kuma an yi mata rajista a karkashin hukumar kula da harkokin addini ta jihar Kano.

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »