Tarihin Sheikh Aliyu Rashid Makarfi

0 693

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Aliyu Rashid Makarfi An haifeshi a garin makarfi karamar hukumar Makarfi dake Jahar Kaduna Nigeria ya taso a wajen mahaifin su wanda a dakin su shine na goma sha daya da haihuwa wajen mahaifiyar sa, yana da yayyai Goma sannan yana da kannai uku.

KARATUNSA NA BOKO.
Yayi karatu a Primary School dake makarfi wanda ya tafi barewa college Zaria inda yayi karatunsa na gaba da Primary ma’ana secondary a Makarantar, Sannan yayi karatu a Nuhu Bamalli Polytechnic Zaria, bayan nan ya wuce Bayero University dake kano.

KARATUNSA NA ADDINI.
Amma yanzu yafi karkata a Harkar Almajiranci na karantar da addini, saboda mahaifinsa Malam Adamu Rashid” shine Malamin Makarantar Islamiyya na farko a garin makarfi wannan ya karamai zumma ta yadda tun tasowarsa yaji yanada sha’awar abinda mahaifin nasu keyi don haka ya maida hankalin sa akan hakar.

A tattaunawa da manema labarai ya bayyana cewa: tun daga wajen mahaifin nasa yake karatu bayan yayi Islamiyya sannan yayi karatu a gaban malamai irin su “Marigayi Sheikh Ahmad Usman Kauru, “Marigayi Na’ibin Zazzau Alkali Mal. Yahuza”, “Marigayi Malam Allu Dake cikin Zaria City” sanna lokacin da yake zaune a kano yayi karatu a wajen “Malam Muhammad Sani Kaka” da malamai sosai wanda har yanzu a lokacin da ake tattaunawan dashi yana daukan karatu a wajen wasu daga cikin malaman nasa.

A hakan kuma yana karatun sai Allah ya taimakeshi yana tafiya da wa’azi karkashin malamai da dama, irin su Marigayi Sheikh Abubakar Ikara, Sheikh Yusuf Sambo Muhammad Rigacikun, kasancewarsa a zaria sai yatashi Gaban “Sheikh Mal. Auwal Adam Albani Zaria” ya basu wata irin hamasa wanda akeba yara matasa, Hakan yasa abin ya kara bashi sha’awa sosai, daga bisani Allah ya taimake shi ya hadu da “Prof. Nuhu Tahir Tajudden” wanda suke tafiya karkashin kungiyar IZALATUL BIDI’A WA IKAMATUS SUNNAH, suka sanyasu cikin jagorori har shuwagabannin dake cikinta suka daukesu suka basu jagoranci har ya zamto a yanzu shine Secretary na kwamitin Masallatai na Kasa, bayan yaayi shugabancin matasa a Jahar Kaduna.

ABIN DA KE DAMUNSA KUMA YAKESO A RAYUWARSA.

Ya bayyana cewa daga cikin babban abinda yafiso shine hadin kan Alumma, kuma hadin kan Alummar nan yakama tun daga kan a Addinan ce wato ta fuskar addinin musulunci, haka zalika zama ya hadamu da wadanda ba musulmi ba akwai bukatan mu rinka samin zaman lafiya a tsakanin mu, mu mutunta kowa da Addinin sa, mu mutunta kowa da mutuncin sa, wannan zai taimakemu kwarai wajen samin cigaba a rayuwar mu.

ABINDA YAFI SO A CIKIN ABINCI.
Ya bayyana Tuwa na Masara wanda yace yanzu ana yinsa da semon Vita wadda nau’ice ta Alkama a matsayin babban abincin da yakeso amma yanacin tuwon dawa, yanacin tuwon shinkafa, indai abincine yafi so a ransa babu wanda yafi Tuwo, daga baya su shinkafa sai sibiyo baya, amma da yake yayi zaman karkara yanacin nau’ikan abinci kamar su: Danwake, Gauda, Rummace, Barangwaje, Gaigaya, da abincika da dama wanda wasu baza’a sansuba sai wadanda suka zauna a karkara.

ABINDA YAFI KOKARI DA BADA MUHIMMANCI AKANSA.
Ya bayyana cewa ba abinda yafi kokari da bada muhimmanci a kansa kamar Alqur’ani domin kuwa a ka’ida ta addinin musulunci ma duk malamin da zaiyi da’awa matukar bai fahimci Alqur’ani ba zaiyita bankaurane kawai, shiyasa ya maida hankali sosai fannin Alqur’ani har Allah ya taimakeshi dan abinda ya sani yayi laushi tare dashi wanda zaiyi wahala yayi karo da Ayar Alqur’ani yajita bakuwa a wajen sa.

ABINDA KE FARANTA MASA RAI A RAYUWA.
Ya bayyana abinda yake faranta ransa wanda yace yanason yaga iyali suna zaman lafiya ko abokai yadda ko kasuwane ko Masallaci zakaga Mutum ya jero da Iyalinsa domin zuwa ibada ko wani abin hakan ba karamin faranta masa rai yake ba, ko yaga jama’a antaso anzo ana yin abu a dunkule ba a rarrabe ba.

ABUBUWAN DAKE BATA MASA RAI.
Abin da yafi batamasa rai shine yaga ana cin mutuncin wani ko anaso sai an tozarta wanu hakan ba karamin bata ransa yake ba, kuma bayasan girman kai sam a rayuwar sa.

BABBAN BURIN SA.
Babban birinsa na farko yace shine Allah Ubangiji ya bashi kudi na halalinsa wanda zai gina Makaranta da Masallatai ya dan kashi ga al’umma wanda zai rinka gudanuwa karkashin sa wanda ba nashi bane bana yayanshi bane ya dan kashi ne ga alummar Musulmi ayi harkar addini dashi,

Sannam barinsa na biyu akwai yara nashi dana yan’uwanshi da Marayu wadanda yake kula dasu wanda babban burinsa yaga tasowarsu da cigaban su a rayuwa ko da ransa ko babu ransa.

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »