Tarihin Shaikh Muhammad Bello Aliyu Yabo

0 1,564

Muhammad Bello Aliyu Yabo wanda aka fi sani da Bello Yabo, an haife shi a ranar 1 ga watan Janairun 1962, malamin addinin Musulunci ne na Najeriya.

Bello Yabo ya yi makarantar Islamiyya tun yana karami. Bayan ya kammala sai Yabo ya fara karatunsa na firamare a makarantar firamare ta Yabo, daga nan kuma ya wuce makarantar Government Day Secondary School.

An nada Bello Yabo a matsayin mai ba da shawara na musamman kan kula da hanyoyin karkara, ya yi aiki a matsayin mai duba kudi na cikin gida a karamar hukumar Dange-Shuni, Daraktan kudi na musamman na asibitin Sokoto, Daraktan kudi na SUDA da ma’aikatar ilimi ta Sakkwato.

Bello Yabo ya soki gwamnatin Muhammad Buhari kan rashin tsaro a Arewacin Najeriya, (Arewa maso Yamma) musamman a Zamfara, Sokoto, Kaduna, Katsina da Jihar Neja.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »