Takaitaccen Tarihin Sheick Malam Auwal Muhammad Albani Zaria

0 2,049

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

HAIHUWARSA

Sheik malam Muhammad Auwal Albani zaria an Haifeshi a watan (Rabi’u sani shekarata 1379) daidai da 27-September 1960) A cikin unguwar muciya dake cikin zaria, Kaduna state Nigeria,

KARATUNSA

Malam yayi karatuttuka da yawa, ya yi firamary da Secondary a nan Zaria, ya yi karatu a Commercial College Muchia Zaria, ya yi a Hayin Ojo, yayi Barewa College, kai ya ma yi Demonstaration Secondary School dake
cikin A.B.U, kuma ya yi karatu a jami’o’i Hudu a cikin ƙasar nan,

Yayi a jami’ar Ahmadu Bello (ABU), ya yi a jami’ar Jos, ya yi a Jami’ar
Modibbo Adama dake Yola, wacce aka fi sani da FUTY, sannan ya yi karatu a wata wacce ake ce mata Digital Bird Institute, wacce take da alaƙa da (AFFILIATED) da jami’ar Najeriya (University of Nigeria, Nsuka) har dai malam ya rasu ɗalibi ne a ABU yana digiri na biyu (Masters) a “Electrical Electronics Engenering Department”.


Baya ga wannan, malam yayi karatuttuka da na addini, galibin karatun da yayi,sune a Birnin Kano, ya yi karatu a wajen Sheikh Aminudden a Kano, sannan ya yi karatuttukan zaure da yawa, wata rana malam da kan shi yake faɗa mana cewa, mahaifiyar shi ta kwaxaitar mai da cewa tana
so ya zama malami. In zai tafi kano, ita take
qullamai garin rogo ya tafi da shi, sabo da
kada yunwa ta hana shi karatu a can, daga
baya da malam ya fara kasuwanci yana
samun kuxi, malam ya kan sayi tiket na jirgi
musamman dan yaje qasar Saudiyya yayi
karatu. Ya yi karatu gaban Sheikh Uthaimin
karatu sosai, ya yi karatu a wajen Sheikh Al-
gamidy, wanda shi ne tsohon Bursar
(shugaban vangaren kuxi) a jami’ar Madina,
akwai malaman jami’ar Madina da yawa
waxan da malam yayi karatu a gaban su,
amma ba’a matsayin shi na xalibi a jami’ar ba,
a’a, a matsayin shi na xalibi wanda ya kai
kanshi koyon ilimi a wurin su. Wannan shine
tarihin malam abin da ya shafi ilimi a taqaice.

MUTUWARSA

An bayyana cewa ‘yan bindigane suka harbe malamin da iyalin nasa ne lokacin da suke cikin mota suna kan hanyar su ta komawa gida daga makaranta a cikin garin Zaria jihar Kaduna.

Wadanda suka kai masa harin an bayyan cewa suna cikin wata mota ne kuma bayan da suka harbe shi da iyalin nasa sai da suka sake janyo shi daga cikin motar suka kara harbinsa don su tabbatar ya mutu.


Sai dai wasu rahotanni sun ce anan take ne dai uwargidan nasa ta rasu, amma malamin da dan nasa sai bayan an kai su asibitin Wusasa dake garin na Zaria ne rai ya yi halinsa.

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »