Bani Da Lafiya Kashi Na Sabain Da Hudu (74)

0 519

“Ku kyautata zabin abokan zaman aure wadanda za su rika taimaka muku wajan yin Azkaar a ko da yaushe ba dare ba rana, da kiyaye dokokin Allah iya gwargwado, domin samun Allah yakiyayeku da iyalanku da kiyayewarSA kuma ya tsare ku da tsarewarSA daga sharrin Shedanun Mutane da na Aljanu.”

Malamin ya amsa da cewa: Tabbas kam kinyi tambayar da ta kamata kuma insha ALLAH ga malamarku nan mace irin ku za ta yi miki d ma sauran mutane cikakken bayanin yadda yakamata ayi cikin iko da yardar Allah.

Aka baiwa Malama lasafikar magana, bayan ta yi muqaddima tayi sallama kuma aka amsa sai take cewa: Wato na ji dadi da akayi wannan tambayar, dama irinta ne yakamata a rikayi kuma wannan shi ne ke nuna mana kuma yatabbatar man cewa muhadarar nan ana fahimtarta sosai, Allah yasa mudace kuma yakara tsare mana imaninmu.

Malama taci gaba da cewa: Wato sau da dama muna barin gini ne tun ranar zane, domin irin wanna riga-kafin tun a wajan zabar abokin zama ne yakamata a fara yinsa, wajan mutum ya tabbatar ya zabarwa yayansa uwa tagari, itama ta zabarwa yayanta Uba nagari.

Bareerah ta kalli Labeeba sai take cewa: Wato kinga daya daga cikin abinda nake jin tsoro nan nima, domin yana cikin dalilan da suka sanya ni har yanzu banyi aure ba sbd kinga ni ba ni da matsalar jinnu amma kuma matsalar itace wajan samarin da suke zuwa wurina.

Labeeba: Bangane matsalar wajan samarin da suke zuwa wurinki ba, kina nufin ba kyason su rika zuwa ne ko yaya?

Bareerah: Allah Sarki yar uwa, ai ina nufin har yanzu wadanda suke zuwa wuri na gaskiya ban yarda da rikonsu da Addini ba kuma ban yarda da tarbiyyar su ba gaskiya, saboda ina jin tsoron naje nayi kitso da kwarkwata saboda ni kadai abin zai shafa ba wacce tayimin kitson ko yan kallon kitson ba.

Labeeba: Maasha ALLAH, tabbas kam wanna bayanin na ki haka yake, gwara mutum yayi iya kokarinsa wajan yaga ya kyautata zabin wanda zai zama Uban yayansa, saboda samun nagartattun zuriya wadanda Al’umma za suyi farin ciki da alfahari da su.

(Insha ALLAH za muji ci gaban wannan bayanin a rubutu nagaba.)

Allah yasa mudace Kuma yakara mana lafiya mai amfani.

Har kullum mu rika tabbatarwa da zuciyar mu cewar: Magani sila ne na waraka amma ba shi da ikon warkarwa, Allah ne kadai mai iya warkar da wanda yaga dama a duk lokacin da yaga dama, shi kadai ne abin dogara ba maganin ba.

(Ayi mana Addu’ar ALLAH ya yarda da mu da ayyukanmu kuma ya lullube mu da RahamarSA.🤲🏻)

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »